Kungiyar Manoman Auduga ta kasa (NACOTAN) ta shekanta cewa, sakamakon daukin da Gwamnatin Tarayya ta samar a fannin noman Auduga a kasar, hakan ya sa, adadin manoman Auduga sun karu daga 90,000 zuwa kusan 134,000 daga kakar shekakar 2018 zuwa kakar shekarar 2020
Tun shekara ta 2018, noman auduga yana kan hanya mai zuwa biyo bayan daukin da Gwamnatin Tarayya ta samar na daga darajar noam Auduga ya fadin kasar nan.
Manoman auduga sun ce matakin samarwar da ake yi a yanzu yana da nasaba ne da ingantawar da aka samu ta hanyar samar da iri mai inganci da kuma katsalandan din da gwamnati ta yi a yankin.
Tun daga shiga tsakani, adadin manoma sun karu daga 90,000 a 2018 zuwa kusan 134,000 don daminar shekarar 2020.
Shugaban kungiyar Manoman Auduga ta kasa Mista Anibe Achimugu ne ya sanar da hakan a hirar da aka yi da shi a Abuja.
Mista Anibe wanda kuma shi ne Manajan Daraktan Arewa Cotton ya bayyana cewa, ana sa ran noman audugar za ta haura tan 200,000 a daminar shekarar 2020, ya kara da cewa, a shekarar 2019, manoman audugar sun cimma 120,000 zuwa 130,000 tan wanda ya kai kimanin tan 80,000 ya karu.
A cewar Mista Achimugu, akwai kimanin kamfanoni takwas na a cikin shekarar 2019, kuma a yanzu haka, lambar ta kusa zuwa gidajen mai 25 tare da karin wasu a karkashin shirin aikin noma na Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Ya bayyana cewa, daukin da bakin CBN ya yi a kakar 2019 ya magance sauya shigo da da kayayyaki daga kasashen waje, inda ya kara da cewa, Audugar da aka samar ta biyo baya wadanda aka sarrafa sun fi karfin abin da kamfanonin masakun Nijeriya zai iya cinyewa a yanzu.
Ya ce, abin da CBN ke kokarin yi da yawan abin da muke da shi a layin auduga da aka samar shi ne don fitar da shi ta yadda zai kara karfin samun canjin kudaden musaya na kasashen waje.
A cewarsa, amma ko da a matakin farko na sarrafawa, kun ga cewa za mu iya jawo hankalin gwamnatin tarayya ta fadada hanyoyin samar da kudade.
A kan farashin ta a yanzu Shugaban NACOTAN, Mista Anibe Achimugu ya ce, farashin auduga na yanzu ya kasance mafi kyau da manoma suka samu damar jawowa a kowane lokaci har iya tunaninsa.
Shugaban Mista Anibe Achimugu ya ci gaba da cewa, na san cewa a shekarar 2019, farashin kowace tan a kan Naira 205,000 ga manoma, ya ci gaba da cewa, hakan na nufin manomi yana samun riba sama da Naira 100,000 kai tsaye cikin aljihu idan har zai iya samar da tan biyu na auduga iri.
Shugaban Mista Anibe Achimugu ya kara da cewa, wannan daukin na bakin ya kasance kamar yadda CBN ke son fara harkar.
Ya kara da cewa, ba shakka, kuna so ku bar shi zuwa wani karin fadada farashin kasuwa da bukata, kuma a yanzu, mafi karancin farashin a wannan shekarar, shine Naira 185 , 000 na kowanne tan, wanda har yanzu ya fi kyau idan za a bar shi da kansa.
A cewar Shugaban Mista Anibe Achimugu, farashin ya kasance Naira 140,000 zuwa Naira 150,000 a kowanne tan, inda ya kara da cewa, ina ganin mafi karancin farashin da aka bayar da tabbaci tunda sa bakin ya yi kyau.
A kan ingancin iri na Audugar Shugaban NACOTAN, Mista Anibe Achimugu ya ce, manoman auduga sun ce a cikin shekarar 2019 sun samu ingantacciyar hanyar samar da ingantaccen iri tare da samun yawan tan 2.5 a kowace kadada idan aka bi hanyoyin da suka dace.
Mista Achimugu ya ce, “Wani manomi yana tsalle a yawan amfanin gona da ya kai tsakanin kilo 400 zuwa 500 a kowace kadada wanda a wancan lokacin ya kai kimanin 1.2, 1.5, kuma a zahiri, wasu na samun tan 2.5 a kowace kadada”.
Ya kara da cewa, daukin da gwamnatin tarayyar ta samar a fannin na noman auduga a kasar nan, hakan ya kara bunkasa fannin da kuma kara inganta sana’ar.
A kan fitar da audugar da ta wuce gona da iri, Achimugu ya ce, kamar yadda nake magana da ku, muna da kamfanonin kasuwanci na duniya da suke da sha’awa, kuma na san galibi idan suka tura audugarmu ta Nijeriya zuwa kasashen bangladesh, China da Indiya.
Noman Kashu Na Taimaka Wa Fannin Tattalin Arziki, Cewar NCAN
kungiyar masu noman Kashu ta kasa (NCAN) ta yi kira...