Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NOMA

Noman Bana: Ci Biyu A Gonar Dadin Kowa, Masara Sau Biyu Shinkafa Sau Biyu

by Muhammad
February 21, 2021
in NOMA
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Zainab Garba Danammani,

Bismillahir rahmanir Rahim, da sunan Allah mai rahma mai jin kai.

Dukkan yabo ya tabbata ga ubangijin talikai, mai kowa mai komai, mai kuma ajiye komai a muhallinsa. Da farko ina yi wa Allah (S.W.A) godiya bisa ni’imar da ya yi mana baki daya musamman mu manoma, domin noman bana babu abinda zamu ce ma Allah saidai mu ce mungode bisa wannan ni’ima ta sa, hakika noman bana ta yi kyau fiye da yanda mukai tsammani, munyi noma daga farkon damina zuwa karshe lafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba, musamman a yankin mu na Funtua, mun kuma samu alkhairi matuka yayin da muka girbe su waken suya, masara, dawa da kuma farin wake, saboda haka babu abinda zamu cewa Allah sai godiya, Allah kuma ya kara kare manoma da dukkan al’umma baki daya daga firgici da tashin hankali ya kara kare mu da kariyar shi baki daya.

Sabanin wadancan lokuta na baya da a ka sha fama a bangaren rashin tsaro, a inda manoma sukai ta fama da fargaba na ta’addanci daga miyagun ‘yan bindiga, boko haram da kidnappers, to Alhamdulillah lallai mun samu sauyi na tsaro kwarai da gaske, saboda haka muna masu godiya ga Allah (S.W.A) bisa kariyar shi a gare mu baki daya, sannan muna godiya ga shuwagabannin mu wanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin tsaro ya tabbata a kasar mu nijeriya, mun gode.

Manoma shalelen Allah, taki yazo gida, na tanadar maku takin gargajiya wato kashin shanu, kashin tumakai, kashin awakai da kuma kashin kaji, nesa tazo kusa zaka ga tambari na a buhunna na, hoton masara da dawa, a saman buhun akwai suna kamar haka  “Dadin Kowa Form one, Sarauniya Gimbiya one, edcellent local fertilizer and specialize in any types of goods production and building construction” zaka ga prize a rubuce N2000 kacal babu mis, babu algushu ko kasa ko yashi, sayan nagari maida kudi gida, sai an gwada a kan san na kwarai, zubi daya shekara uku.

Gonar dadin kowa farm gona ce da Allah ya albarkata wacce ta kafu da tsarin Allah wato zakka, saboda haka ina kira ga yan’uwa na manoma da su kara kaimi wajen bayar da zakka domin kuwa taken Allah shine zakka, yana daya daga cikin babban sirrin wannan gona tawa ta Dadin Kowa Farm, a inda na tashi tsaye ba dare ba rana wajen ganin na tabbatar da ita domin talakawa da mabukata su amfana, don haka ina kira ga manoma da su bayar da zakka muna kira da babban murya ga manoma dasu bayar da zakka. Sannan harwala yau kuma ina kira ga manoma da ‘yan kasuwa da su sauko da farashin abincin su domin amfanin talaka musamman a irin wannan mawuyacin hali da muka tsinci kanmu, kamar yadda Allah (SWA) ya ke cewa ku bani kalilan sai na maida maku da kasiran, saboda haka duk da halin da muke ciki ya kamata muma a samu sassauci daga gare mu iya bakin gwargwado, duk da ya ke ureya da kanfa sunyi tashin gwauron zabi amma kuma takin Baba Buhari ya taimaka.

Nasiha ga manoma, ina roko ga duk wani manomi dake fadin kasar nan da a bar zagin shuwagabanni tun daga shugaban kasa, sarakuna, gwamnoni, da duk wanda Allah ya zaba babu zagi tsakani sai addu’a in baka iya addua’ kayi shiru domin zagin kai talaka yake dawo mawa ka lalace ‘ya’yan ka su lalace.

Gonar dadin kowa tana cikin saika gani ta marigayi Garba Danammani a garin dakamawa da ke Karamar Hukumar Funtua a jihar Katsina, wacce a yanzu itace gonar mai martabiya, sannan kuma sai kanwar ta Balaraba, wacce na ta gonar ke garin mai ruwa.

Gonar Dadin kowa ta samo asali ne tun daga mahaifin mai martabiya, wato Garba Danammani wanda bayan koma wanshi ga mahalicci sai ita sarauniya ta gaji wannan gona ta Dadin Kowa Farm.

Garba Danammani Funtua mutum ne jajirtacce musamman a harkar noma, wanda a duk fadin garin Funtua babu manomi kamarshi, sannan yayi fice wajen taimakon al’ummar Annabi ta hanyar taimaka wa talakawa da gajiyayyu da kayayyakin gona  da kuma bayar da zakka ga talakawan garin Funtua da ma wasu garuruwan da ke kewaye da su, ya kuma horas da matasa ta hanyar basu ayyukan gona da filayen noma da kuma rarraba masu zaruruwan dinki dama wasu ayyukan  daban-daban domin su dogara da kawunan su.

A karshe kuma ina mika godiya ta cikakka da kafuwar ita wannan gona mai albarka mai kuma dumbin tarihi ta Dadin kowa wanda zamu ce tun bayan rasuwan mahaifi na marigayi Garba Danammani Funtua, Allah ya mai gafara, manomi ne babba kuma rikakke wanda kowa ya sani a Nijeriya babu manomi da yayi noma a Nijeriya kamar wannan bawan Allah, saboda haka mai martabiya ta dauki nauyi da irin dashen da yayi mata a kan abinda ta ke kai, saboda haka nema a yau noman da a ke yi a ita wannan mashahuriyar gona ta Dadin Kowa babu inda a ke irin ta a nan kusa a Nijeriya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kayan Da’a Na Mata: Illa Ko Amfani? (3)

Next Post

Martani: Hukumomin Gwamnatin Tarayya Sun Kashe Naira Biliyan 3.77 Wajen Tafiyarsu Da Iyalansu Saudiyya

RelatedPosts

Karo

Gwamnatin Tarayya Za Ta Cigaba Da Samar Da Ingantattun Irin Karo – Minista Shehuri

by Muhammad
18 hours ago
0

Gwamnatin Tarayya ta shelanta cewa, za ta ci gaba da...

Karo

Yadda Za A Kara Fadada Noman Karo A Nijeriya -UNCTAD

by Muhammad
3 days ago
0

Daga Abubakar Abba, Taron sashen Majalisar Dinkin Duniya kan kasuwanci...

Musa Malumfashi

Abin Takaici Ne Yadda Nijeriya Ta Fifita Danyen Mai Kan Noma – Kwararre

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Obiora Madu, Darakta Janar na Multimid, ya sanar da cewa,...

Next Post
Gwamnatin Tarayya

Martani: Hukumomin Gwamnatin Tarayya Sun Kashe Naira Biliyan 3.77 Wajen Tafiyarsu Da Iyalansu Saudiyya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version