Connect with us

LABARAI

Noman Damina: Gwamnatin Kebbi Ta Kaddamar Da Kwamitin Taki

Published

on

Gwamnatin jihar Kebbi, a jiya ta kaddamar da kwamitin sayar da Taki na shekara ta 2020 domin noman damina a dukkan kananan hukumomin 21 na jihar ta Kebbi .
An kaddamar da kwamitin ne a fadar gwamnatin jihar ta kebbi da ke a Birnin-kebbi a jiya, domin kula da rabawa da sayar da Takin ga manoma na dukkan kananan hukumomin jihar da kuma tabbatar da cewar samun Taki wadatacce a cikin jihar ta Kebbi ba tare da wata matsala ba.
Haka kuma Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu, yayin da yake kaddamar da kwamitin sayar da Taki a jihar a madadin gwamnatin jihar Kebbi ya ce, “Gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, ta kaddamar da wannan kwamitin ne domin tabbatar da samuwar wadataccen Taki a duk fadin jihar ga manoma, in ji shi.”
Har ilayau, ya ci gaba da cewa “Gwamnatin jihar ta shirya tsaf domin kara bunkasa harakokin noma a jihar da kuma kasar Najeriya bakidaya. Saboda gwamnatin jihar na kokarin ta na ganin cewar ta farfado da tattalin arzikin jihar da na kasa ta hanyar noma, in ji shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar ta Kebbi”.
Bugu da kari, ya bayyana sunan shugaban kwamitin da kuma na sauran mambobin wadanda suka hada da Alhaji Abubakar Bello, a matsayin shugaban Kwamitin, Barista Abubakar Zaki Lonzon, a matsayin Sakataren Kwamitin sai kuma Alhaji Abubakar Bello Bunza, a matsayin mamba.
Sauran sun hada da Alaramma Atiku Warah, Alhaji Musa Muhammad Argungu, Alhaji Danladi Jandusti da kuma Alhaji Mohammed Zaure Sakaba. Hakazalika ya ce” ayyukkan da aka bukaci Kwamitin ya gudanar sun hada da sayar da Taki, sanya kudade a cikin asusun gwamnatin jihar, samar da wadatacen Taki a jihar da kuma kula da littafin sayar da kudaden Taki da kuma raba Takin ga manoman jihar ba tare da wani koke ba da sauransu.
Daganan shugaban ma’aikatan na fadar gwamnatin jihar ta Kebbi, Suleiman Muhammad Argungu, ya bukaci Kwamitin da su yi amfani da ilminsu da kwarewar da aka sansu da ita kan harkokin noma wurin tabbatar da cewar sun gudanar da ayyukkansu yadda ya kamata ba tare da samun wata matsala ba.
Ya ce”Manoma za su iya samun Taki na gwamnatin jihar Kebbi a kan kudi Naira dubu 5,500 a kowane buhun Taki daya a hannun wannan kwamitin da aka kaddamar a jiya domin saya.
Harwayau, za a iya samun wananan Taki a kowace karamar hukumar mulki na duk fadin jihar , in ji Suleiman Muhammad Argungu.”
Haka kuma daga karshe ya yi kira ga manoman na dukkan fadin kananan hukumomin jihar da bai wa Kwamitin goyon baya domin su iya gudanar da ayyukkansu cikin sauki .
Advertisement

labarai