Abubakar Abba" />

Noman Kashu Na Taimaka Wa Fannin Tattalin Arziki, Cewar NCAN

kungiyar masu noman Kashu ta kasa (NCAN) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya data wanzar da tsarin noman Kashu a kasar nan, musamman ganin cewar fannin yana samar da dimbin kudade ga kasar nan.

Har ila yau, kungiyar masu noman Kashu ta kasa ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta samar da dabaru wajen zuba jari mai dimbin yawa a fannin.
Shugaban kamfanin Mangro Cif Oke Okoroafor wanda kamfanin nasa ya kasance akan gaba wajen zuba jari a fannin noman cashew a yankin Kudu Maso Yamma ne ya yi kiran a lokacin da aka gudanar da zaben sababbin shugabannin kungiyar ta NCAN a garin Lokoja reshen jihar Kogi.
A cewar Shugaban kamfanin Mangro Cif Oke Okoroafor, fannin aikin noma yana taimakwa matuka wajen habaka tattalin arzikin ko wacce kasa dake a fadin duniya.
Shugaban kamfanin Mangro Cif Oke Okoroafor ya kuma yi kira ga daukacin gwamnatocin da ke kasar nan, su mayar da hankali wajen bunkasa fannin na noman Kashu .
Shi ma a nasa jawabin a wurin taron, Shugaban kungiyar na kasa Mista Ojo Ajanaku ya sanar da cewa, kungiyar anyi mata rjista ne a shekarar 2004, sai dai bata samu damar gudanar da ayyukan yadda yakamata saboda wasu yan matsaloli.
Shugaban kungiyar ta NCAN na kasa Mista Ojo Ajanaku ya kara da cewa, hakan ya zamowa kungiyar matsala wajen habaka fannin na noman cashew da kuma samun damar zuba dimbin jari mai yawa a fannin na nomansa.
Shi kuwa Fasto Isaac Ojonugwa, wanda ya wakilci kungiyar masu amfanin gona ta kasa (FACAN) ya sanar da cewa yazo jihar ta ne don sanya ido kan yadda za a gydanar da zaben na sababbin shugabannin kuniyar ta NCAN.
Alhaji Ibrahim Siaka Duche ne aka zaba a matsayin sabon shugaban kungiyar ta NCAN reshen jihar, inda kuma Jibrin Haruna aka zabe a matsayin mataimakin shugaba.
Sauran su ne, Muhammed Yakubu wanda ya zamo Skatare sai Alhaji Ademu Makama, a matsayin mataimakin shugaba na Kogi ta yamma sai Abejirin Johnson, a matsayin mataimakin shugaba na Kogi ta tsakiya Audu Zubair, mataimakin shugaba na Kogi ta tsakiya sai Ahmed Igonoh, a matsayin ma’ajiyi sai kuma Abdulrahim Haruna a matsayin mataimakin ma’ajiyin kungiya da sauransu.
A wata sabuwa kuwa, wani kamfani ya samar da ingantaccen Irin na Tumatir da kamfanin Teryima ya samarwa da manoman Tumatir a jihar wanda yace, yasha ban-ban da sauran da aka shafe shekaru ana shukawa a jihar.
A cewar Manajin Daraktan kamfanin na Teryima Tarnongu, sabon Irin na Tumatir zai samar da manyan Tumatir dake dauke da ruwa dan kadan ya kuma jima a ajiye feye da wanda aka sani na gida har ya kai lokacin nunar sa ba tare da ya rufe ba.
A cewar Manajin Daraktan kamfanin na Teryima Tarnongu, sabon Irin kuma yana karawa Tumatir lafiya da kuma samar da dandano mai dadi, inda hakan zai dinga jan ra’ayin masu saye ba kamar na Irin tsohon Tumatir da ake samarwa a jiharta Biniwe ba wanda ba a iya sayarwa da masu bukata ba.
Shugaban ya kuma yi kira ga Gwamnatin jihar ta kammala aikin masana’antar sarrafa Tumatir da ke yankin Wannune a cikin karamar hukumar Tarka wacce tsohuwar Gwamnatin Gwamnan jihar Sanata George Akume ta fara ta kuma yi watsi dashi.
A cewar Manajin Daraktan kamfanin na Teryima Tarnongu Joji, in aka kammala aikin masana’antar ta sarrafa Tumatir, za ta taimaka matuka wajen rage asarar da manoman sa a jihar suke tabkawa za ta kuma bai wa manoman jihar kwarin gwaiwar noma Tumatir nai dimbin yawa a jihar ds samar ds ayyukan yi ga yan jihar, musamman matasa.
Shi ma a na sa jawabin, Ma’ajiyin kudin kungiyar reshen jihar Mista Emmanuel Kugba ya bayuana cewa, manoman Tumatir a jihar a yanzu, an samar masu da ingantaccen Irin na Tumatir don yin noman sa a kakar noman rani na bana.
A cewar Ma’ajiyin kudin kungiyar reshen jihar Mista Emmanuel Kugba, dukkan wani taimako da manoman na Tumatir a jihar suke bukata, kamfanin ya samar masu.
A nasa jawabin tunda farko Babban Jami’I a kamfanin na Teryima Injiniya Msughter ya ce, hadakar da kamfanin ya yi da kungiyar ta manoman Tumatir reshen jihar Biniwe, ya shirya zasu noma Tumatir akan kadada 31 a kananan hukumomi uku na Buruku, Ushongo da kuma a Makurdi.
A cewar Babban Jami’I a kamfanin na Teryima Injiniya Msughter, aikin ana sa ran a kalla a samar da tan 100 na Tumatir a cikin ko wacce kadada daya, inda kuma Babban Jami’I a kamfanin na Teryima Injiniya Msughter ya kara da cewa, shi yasa kamfanin ya yanke shawarar taimakawa manoman na Tumatir da ke jihar ta Biniwe.
Babban Jami’i Injiniya Msughter ya kara da cewa, wannan aikin shine karo na farko da kamfanin ya taimaka wa manoman Tumatir a jihar, inda ya kara da cewa, mun kuma rabar da Irin Tumatir ga mamoman Tumatir a jihar yadda za a kara samar da ingantaccen Tumatir a jihar.

Exit mobile version