Connect with us

NOMA

Noman Masara

Published

on

Masu karatu barkan mu da sake saduwa a wannan fili namu na Noma Tushen Arziki da fatan ana fahimtar da Karuwa daga abubuwan da muke tattaunawa a wannan fili namu, Allah Ya sa mu dace amin. A wannan mako za mu yi bayani ne a kan wannan amfanin gonar mai daDaDDen tarihi, mai gina jiki da kuma juriya daga Kwari. Bincike ya tabbatar da ana girbe sama da tan Miliyan 800 na wannan amfani gona a faDin duniya sannan mutane fiye da Miliyan 500 ke cin masara a matsayin abinci a faDin Afirka a duk shekara. Samun muhimman wannan amfani yanzu za mu tattauna ne a kan asali da takaitaccen tarihin masara, yadda ake nomanta musamman a wannan yanki namu na Arewacin Nijeriyar nan da kuma alfanun da ke tattare da wannan amfani gona mai tsohon zamani.

 

TAKAITACCEN TARIHI

Masara tana daga dangin ciyayin nan da ake kira da Genius poecae, wanda suka Kunshi fiye da kala dubu na ciyayi. Masara kamar yadda muka sani tana da yanayi na hatsi kamar Alkama da Dawa da sauran su. Hujjojin kimiyyar aikin gona sun tabbatar da cewa yabanyar da a yanzu muka santa da Masara an fara gano tane  wajen shekaru 7,000 kafin haihuwar Annabi Isa da suka shuDe, daga cikin ganyayyakin dajin nan wato Toasinte. Masarar yanzu ta sha bamban da ta waccan zamani domin kuwa kusan har yawancin manoman muna yanzu ba na tsammanin sun san cewa, waccan masara ta dauri ta fi ta wannan zamani KanKanta da DanDano ba kamar irin ta yanzu ba. Haka abin ya ci gaba da tafiya har zuwa shekara ta 1500 kafin haihuwar Annabi Isa, inda Turawan daji (mesoamerican) suka zamanantar da masara ta hanyar amfani da dabarun noma zuwa yadda muke ganin ta a yau. A Karni na 16 zuwa na 18 ne, noman Masara ya bunKasa ya shiga dukkan sasannin duniya sakamakon mulkin mallakar Turawa, wannan ya sa suke kai  irin Masara nahiyoyi da dama kuma ya samu damar karBuwa ga kusan dukkan mutane.

 

AMFANIN MASARA

KaDan daga cikin amfani da ake da masara shi ne ana sarrafa ta, a mai da ita gari don yin tuwo ko kunu da sauransu, idan an tankaDe ta tsakin ana bai wa dabbobi a matsayin abinci ko zazzagawa su yi fate da ita. Haka nan masana’antun maganin zazzaBi ma suna amfani da masara domin haDe-haDen magungunan su da kuma kamfanonin lemuna da makamantansu.Ba haka nan kaDai ba kamfanonuwan tufafi ma suna amfani da masara wani zubin a madadin roba.

 

ADADIN NOMAN MASARA

Bincike ya tabbatar da Masara ita ce amfanin gonar da aka fi noma wa  a duniya, adadin da ake noma wa kamar yadda hukumar noma da abinci ta majalisar Dinkin duniya ta wallafa a shekarar 2005 ya nuna ana noman masara da ta kai tan miliyan 692 a duniya. Kasar Amurka inda aka fi noman masara suna noma kashi 40 cikin 100 sauran Kasashen da suke mara mata baya sun haDa da Cana da Meziko da Indunusiya da Indiya da Faransa da kuma Ajentina. Binciken baya-bayan nan ya nuna ana noma tan miliyan 817 na Masara a duniya inda ake noma kadada miliyan 159.

A bu na farko wanda na san duk manomin masara ya san wannan shi ne dole kowace gona da za a yi noman masara a cikinta ya kasance a tudu take wato ma’ana ba ta riKe ruwa ko kuma da an yi ruwa nan da nan za ta shanye shi a Dan lokaci Kalilan, sannan ya kasance gonar ta zama tana Dauke da albarka wato (nutrient) wanda za su ba wa irin masara taimako wajen saurin fito wa. Ke nan mun fahimci cewa, noman masara ba a kowace gona ya kamata a yi ba, dole sai an bincika an samu wadda ta cika waDannan siffofi da muka ambata a sama. Masana sun raba masararmu zuwa gida biyu kamar haka;

 

(1) MASARAR ZAMANI : wato wadda muke ganin ta da farin jiki ko yalo iri masarar zamani tana da yalwa sosai domin manomi yakan girbi masara da takai Tan 3 zuwa 7 a duk kadada Daya bayan haka kuma tana da saurin fito wa. Domin kuwa daga fitowarta ba za ta kwana 100 ba za ta Kosa ga kuma juriya daga Kwari da cututtuka kuma ko da a kwari ne a kan iya shuka ta kuma ta fito.

 

(2) MASARAR GARGAJIYYA: Masararmu ta dauri tana da iri kala-kala kuma a kan haData da sauran amfanin gona kamar wake da gyaDa da sauransu, sannan tana ba da amfani mai yawa in aka girbe.

Lokutan shuka masara a wannan yanki namu kamar yadda muka sani shi ne wannan yanki namu kamar yadda mu ka yi bayani a baya cewa damunar mu ba ta da tsayi shi ne nake ganin zan ba wa manomanmu na masara shawarar cewa daga watan huDu zuwa na biyar su tabbatar sun shuka masarar su domin masarar ta Kosa da wuri kamar yadda muka fada a baya. Sannan a kiyayi yin noman masara a Kasan inda itatuwa suka lulluBe don a kaucewa lullumi wanda yake zama illa ga girma da Kosawar masara.

Masararmu ta gargajiyya mai kalar ja da fara za a shuka irin ta mai nauyin kilo 18 a cikin kowace kadada Daya. A kan sa Daya ko biyu cikin kowane rami. Sannan yana da kyau a bar ratar kamu uku a tsakanin kowace shuka. Yayin da masarar zamani kamar yadda masana suke bayar da shawara cewar ya kamata a dinga barin ratar santimita (centimeter) 90 yayin da tsakanin kunya zuwa kunya a dinga barin santimita 34. Ana buKatar iri mai nauyin Tan 25 a kowace kadada Daya inda za a dinga sa iri biyu a duk rami Daya.

Abu na gaba shi ne taki, to masara a kan watsa mata takin zamani ko na gargajiyya. Manomin masara kan iya watsa taki a gonarsa kafin ya yi shuka ko kuma bayan ya yi shuka, a lura cewa ba kowane taki na zamani ko na gargajiyya ba za a watsa a gonar masara ba wato ya kasance an tantance wane taki ne zai fi dace wa ga masara.

Masara na buKatar nome ciyayin da suke kusa da ita kafin ta girma, sannan ana yi mata feshin maganin Kwari domin kare ta daga ilolin da ke tattare da Kwari.

 

Matsalolin Da Ke Tattare Da Noman Masara

Wasu daga cikin matsalolin da ke fuskantar harkar noman Masara a Nijeriya da ma wasu Kasashen Afirka sun haDa da rashin Kware wa, sau da yawa mutane kan faDa monan masara ne ba tare da sun nemi ilimin yadda ake noman ba, lallai komai ka gani yana buKatar ka san yadda ake gudanar da shi. Matsalar rashin issashen jarin kuDi na takura yin naman masara yadda ya kamata cibiyoyin bayar da basussuka kan Dora ruwa mai yawa da tsauraran sharuDDoDi ga masu neman bashin noma haka kuma na kawo cikas a harka noma a Afirka, matsalar wajen ajiya da tsarin da ake bi wajen ajiyar na Kara zama babban tarnaKi ga noman Masara. Barnar Kwari da sata daga mutane na talauta abin da aka girba, rashin cikakken kasuwa da farashi mai kyau shi ma yana karya Kwarin gwiwar masu sha’awar noman masara.

 

 

Advertisement

labarai