Daga Sabo Ahmad, Zariya
Tsohon shugaban ƙasa, Chief Olusegun Obasanjo, ya faɗa ranar Alhamis ɗin ta gabata cewa, noman shinkafa ya fara bunƙasa a Nijeriya tun daga shekara ta 1979, lokacin da ya zama shugaban ƙasa ƙarƙashin mulkin soja, kafin lokacin mulkin shugaban ƙasa Alhaji Shehu Shagari, a jamhuriya ta biyu.
Obasanjon ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a matsayinsa na babban baƙo mai jawabi a wajen ƙaddamar da kamfanin casar shinkafa na Okun Rice, a garin Abeokuta, ta jihar and Ogun.
Obasanjon ya alaƙanta koma-bayan da aka samu a kan harkokin bunƙasa noman shinkafa a ƙasar nan da rashin ɗorewar gwamnati, wanda ya ce, gwamnatin da ta biyo bayan gwamnatinsa ita ce ta Alhaji Shehu Shagari, wadda maimakon ta ƙarfafa tsarin da ya bari na ƙoƙarin bunƙasa noman shinkafar, sai ta naɗa kwamitin da zai dinga shigo wa da ita daga waje. Ya ce, rashin ci gaba da wannan tsarin da ya bari na hanyoyin bunkasa noman shinkafar ya jefa manoma cikin tasku, domin maimakon a sayi shinkafar cikin gida, yadda manomanmu za su samun ƙarfin gwiwar ci gaba da noma ta, sai aka koma sayen shinkafar ƙasar waje.
Obasanjon ya jijina wa shugaban kamfanin casar shinkafar Mista Biodun Onalaja, bisa jajircewar da ya yi wajen ganin wannan aiki ya ci gaba da gudana, wanda yin hakan ba abu ne mai sauƙi ba. Saboda haka, sai ya ƙara da cewa, yana kallon Onalaja a matsayin gwarzo, wanda ya samu nasara a kan harkar bunƙasa noman shinkafa a ƙasar nan. Sannan ya ce, da ƙasar nan za ta samu mutum 100 irin su Onalaja da ta zama mai dogaro da kanta a noman shinkafa, har ma ta zama tana kai wa ƙasashen waje.
A ƙarshe, Obasanjo ya roƙi bankuna da su tallafa wa manoma da bashi, ba tare cajin kuɗin ruwa mai yawa ba, yadda manoman za su iya biyan kuɗin da suka ranta cikin sauƙi.