Daga Abubakar Abba
Bankin Manoma na ƙasa( BOI) ya sanar da cewa Najeriya ta ajiye sama da Dalar Amurka Miliyan 600 dai-dai da Naira Biliyan 216 ba sakamakon haɓɓosan da aka yi wurin noman shinkafa a cikin gida, kuma ba tare da dogaro da Shinkafar da ake shigowa da ita daga ƙasar Thailand da sauran ƙasashe ba. Wannan duk ribar inganta noman shinkafa ta gida ne ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya na noman shinkafa.
Babban Daraktan Bankin na sashen mulki da kuɗi, Niyi Akenzua ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci tawagar mahukuntan Bankin ziyara fadar gwamnan Jihar Oyo Abiola Ajimobi.
Akenzua ya ce, ya kamata a jinjina wa ƙasar nan a bisa maida hankali da ta yi wajen faniin mai har da kuma ƙara ƙaimi wajen farfaɗo da harkar aikin noma.
Akenzua ya ce ya zama wajibi a bayyana goyon bayan da jihohi ke bada wa akan shirin na noma shinkafa na gwamnatin trayya, inda yace, sakamakon hakan ya tasmo da ƙasar daga shigo da shinkafa.
Ya shawarci gwamnatin jihar ta Oyo da ta shiga sahun tsarin na noman shinkafa na gwamanatin tarayya, inda ya ce, “mun kuma ƙara faɗaɗa shirin ga masu buƙata.”
Babban Daraktan ya bayyana cewar daga ɗaya zuwa biyu na kamfanoni masu sarrafa shinkafa dake ƙasar Thailand, sun rufe saboda Najeriya ta daina shigo da shinkafarsu.
Acewar shi,“ ada muna kashe Dalar Amurka Biliyan 22 don shigo da shinkafa daga ƙasar waje domin mun yi tunani cewar shigo da shinkafar daga ƙasar waje ba zai yi mana alfanu ba.
A nashi jawabin gwaman ya jinjinawa minitan Noma da karkara Cif Audu Ogbeh a bisa canjin da ya kawo a fannin aikin noma.
Ajimobi ya ce jihar kamata ya yi ta zama mai samar da abinci da zai wadaci ƙasar nan, inda ya ce inda shugabanin da suka shige sun ɗauki aikin noma da mahimmnaci da tuni an yaƙi yunwa da haɓaka tattalin arzikin ƙasa da kuma samar da aikin yi musamman ga matasan ƙasar nan.
A ƙarshe ya shawarci sababbin mahukuntan Bankin dasu ci gaba da inganta harkar noma musamman don ƙara farfaɗo da aikin a ƙasar nan.