Connect with us

NOMA

Noman Shinkafa Ya Yi Wa Nijeriya Tsimin Dala Miliyan 800 A Shekara 2– BoA

Published

on

Bankin aikin Noma na kasa (BoA) ya sanar da cewar, Gwamnatin Tarayya ta yi tsimin kimanin dala miliayan 800 don karawa Manoman Shinkafa kwarin Gwaiwa dake cikin kasar nan.
Babban Daarakta na sashen Kudi da Kiyaye asara na Bankin Niyi Akenzua ne ya sanar da ha kan a ranar Laraba data ganbata a taron manema labaraia a jihar Legas kafin zuwan ranar taron ganawa da Mnaona da za’a yi dasu a karkashin shirin (MTFC) na shekarar 2018 da za’a gudanar a ranar 10 ga watan Okutoba a cibiyoyin kasuwanci dake kasar nan.
Kamfaniun dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewar Kmfanin tuntuba na Crenob8 ne ya yi kudurin hada taron, inda taron zai haska Mnaonan dake nahiyar Afrika da kuma basu damar fitar da amfanin Gonarsu zuwa kasar waje, musamman zuwa Kasuwar Dubai da kuma ta kasashen Gabas ta Takiya.
Mista Akenzua ya yaba wa shirin na gwamnati a kan raba kafa a kan yadda zata farfado da tattalin arzikin kasar musammman wajen mayar da hankali a kan aikin Noma, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya kada su bari a barsu a baya wajen rungumar shirin don suma su kasance wadanda zasu amfana.
Ya ci gaba da cewar, gwamnati ta yi wa Bankin na Manoma garanbawul a 2016 yadda bankin zai samu sukunin bayar da taimako a kan fannin aikin Noma da kuma wadata kasar nan da abinci.
Babban Bankin Kasa CBN zai samar da naira biliyan 250 don samar da dauki ga Bankin na Manoma wanda za’a samar da kudin a karkashin shirin aikin Noma da ake kira (Anchor Borrower’s).
Ya ci gaba da cewar, a shekarar 2017, mun rabar da kimanin naira biliyan 100 ga Manoma da kuma sake rabar da kimanin naira biliyan 50 a shekarar s 2018, inda ya kara da cewar, noman Shinkafa ya karu inda har mutane suka fara tunain irin kokarin da gwamnatin take yi tun a farko zuwan shekarar 2019 don dakatar da shigo da Shinkafa a cikin kasar nan gaba daya.
Akenzua ya sanar da cewar an mayar dahankali ne a kan yadda za’a samar daingantacciyar Shinkafar da kuma adanata a cikin Buhunna yadda za a fitar da ita zuwa kasuwannin kasar waje.
A bayanin ta tunda farko Uwargida Bola Oyedele ,wadda ta wakilci Kamfnin tuntuba na Crenob8 ta ce, Dubai ta fitar da abinci na samada dala biliyan biyar a 2017 daga Afirka, inda kuma ake sanya ran ha kan zai karu da kimanin dala 400 nan da shekara takwas masu zuwa.
Oyedele ta shawarci Nijeriya da suran kasashen Afirka dasu yi amfani da dimbin damar wajen fitar da amfanin Gona zuwa kasar waje musamman amfanin Gona na Shikafa, Cocoa Alakama, Msasara da sauransu zuwa Dubai da kuma zuwa Cibiyar Gulf.
A karshe ta ce, wadanda zasu halarci taron zasu samu dimbin ilimi a kan amfanin Gona da yadda ake yin kasuwanci a Dubai da fitar da kaya zuwa kasar waje da kuma sauranbsu.

Advertisement

labarai