Abubakar Abba" />

Noman ‘Strawberry’ A Jos Na Kara Bunkasa – Manoma

Kara samun noman strawberry a jihar Filato da aka samu, hakan ya yi watsi da amannar da daka yi a baya na cewar, amfanin ba zai iya noma shi a Nijeriya ba.

Nijeriya dai ta kasance tana da dimbin dama a noman sa for, muna kuma godiya da samun kyakyawan yanayin noma a kasar.

Tun lokacin da aka fara noma shi a yan shekaru da suka gabata a kasar, ya kasance bai samu karbuwa ba a cikin zukatan wasu jama’ar dake a cikin yankin Chaha dake a jihar ta Filato, amma a yanzu, ya kasanace kusan babbar hanyar samun kudi ga manoman sa dake a yankin na Chaha wanda yake a garin Vom a karamar hukumar Jos ta Kudu dake a cikin jihar ta Filato, inda hakan ya kuma a sanya a yanzu a yankin, manoma kadan ne basa noma shi, sai dai, wasu daga cikin manoman sa a yankin da suka shafe shekaru suna nomansa, suna fuskantar wasu kalubale wajen noman sa.

Wasu daga cikin manon sa a yankin Mista Elbis Choji da Mista Isaac Choji sun shedwa Jaridar Daily Trust cewa, har yanzu suna ci gaba da nomansa da suka fara yi tun daga shekarar 2016, inda suka kara da cewa, harta kaisu ga kara fadada gonakan su don ci gaba da yin nomansa a yankin.

Shi ma mahaifin Elbis, mai suna Mista Christopher Choji, wanda kuma ma’aikacin gwamnati ne daka da zama a babban birnin tarayyar Abuja, shima ya rungumi yin nomansa kuma da alamun, ya na samun to ciniki a kasuwar da a kaiwa don ya sayar da amfanin da ya noma.

Sai dai, Mista Christopher Choji ya kuma koka kan yadda tsadar takin zamani da kuma tsadar magungunan kashe kwari magungunan ke zame masu kalubale kan sana’ar tasu, inda ya kara da cewa, hakn yafi zamowa babban kalubale musamman ga manomansa kanan.

A cewar Mista Christopher Choji, baya ga tsadar ta takin zamani da kuma na magungunan kashe kwarin, ban ruwa ma yana zamowa manomansa kalubale da kuma sauran kalubale da mamonsa suke fuskanta.

Mista Christopher Choji, ya ci gaba da cewa, mafi yawanci manomansa sunfi dogara ne ga matan da su ke zuwa saye don yin tallansa a kam manyan hanyoyin garin product Jos.

Mista Christopher Choji, ya kara da cewa, kadan daga cikin manomansa, sukan kai shi zuwa manyan shagunan dale garin Jos da kuma babban birnin tarayyar Abuja.

Wani dalibi da shima ya rungumi nomansa maiy suna Mista Gyang Sunday wanda a yanzu yake kan karatu zango na biyu a kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Filato ya sanar da cewa, ya rungumi yin nomansa ne shekaru uku da suka gabata, inda ya kara da cewa, ribar da yake samu da ita ce yake daukar nauyin karatun sa a Kwalejin.

Dalibin Mista Gyang Sunday ya kara da cewa, gonarsa ta na samar da kimanin Katan hudu a duk sati daya, inda kuma ko wanne Katan daya, nauyinsa ya kai kimanin daga kilogiram 5 zuwa kilogiram shida ya na kuma sayarwa kan Naira 1,000 da kuma sayarwa kan naira 20,000 a duk sati daya.

Mista Gyang Sunday wanda shekarun sa suka kai kimanin 20, ya sanar da cewa, noman nasa ya na taimaka masa sosai kan magance dukkan matsalolin sa na yau da kulkum da kuma iya biyan kudin makarantar sa, sai dai ya koka kan tsadar takin zamani da kuma na magungunan kwari.

Ita ma wata mai sayar da wannan amfanin Polina Abbey ta sanar da cewa, ta na samun kudi ta hanyar sayar dashi da take yi a kan manyan hanyoyin garin Jos, inda Manomiyar Polina Abbey ta kara da cewa,ta na daga cikin mata yan kadan a yankin da take noma shi.

A cewar manomiyar Polina Abbey, tana zuwa gona a dukkan safiya don ta saya a gun manoman da suka shuka shi don sayar dashi kan naira 1000 na ko wanne kilogiram daya.

Polina Abbey ta bayyana cewa, ko nawa ta samu riba hakan yana kara ma kwarin gwaiwa kan sana’ar ta.

Sai dai, manomansa basu da wata bukatar sayen Irin amfanin duk shekara idan zasu yi nomansa, inda suke iya matsar da Irin nasa zuwa wata sabon fili, yadda ba sai sunbsha wata wahala ba wajen nomansa.

Polina Abbey ta sanar da cewa, a cikin yankin akwai dama da yawa ta kadadar yin nomansa wanda kuma kamfanoni zasu iya zuba jarin su a fannin nomansa, musamman don fitar daahi zuwa wasu kasashen duniya don sayarwa.

A karshe Polina Abbey ta koka kan cewa, har yanzu babu wani taimako da suka samu har daga gun gwamnatin jihar ta Filato waddda a cikin sauki zata iya janyo masu zuba jari don sunzuba jarinsuba fannin inda kuma hakan zai kara sanyawa manomansa su kara samun kwarin gwaiwa wajen yin nomansa mai dimbin yawa.

Exit mobile version