Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home NOMA

Noman Zamani: Nijeriya Za Ta Zama Koma-baya Idan Ba Ta Maida Hankali Ba – OFAB

by Sulaiman Ibrahim
March 3, 2021
in NOMA
2 min read
Noman Zamani: Nijeriya Za Ta Zama Koma-baya Idan Ba Ta Maida Hankali Ba – OFAB
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abubakar Abba

Kamfanin kimiyyar kere-kere na Noma (OFAB) dake Nijeriya ya yi bayani da cewa, idan har Nijeriya ba ta gaggauta rungumar yin noma ta hanyar yin amfani da fasahar zamani ba, ba za a barta a baya.
A cikin wata sanarwa da kamfain ya fitar ya sanar da cewa, kasashe da dama, musamman wadanda suka ci gaba a fannin aikin noma suna horar da manoman su kyauta kan fasahar yin nama ta zamani.
Sanarwa wacce babbar jami’a a kamfanin Dakta Rose Gidado ta fitar ta ce, za a iya magance kalubalen samar da abinci a kasar nan ne kawai idan manoman kasar suka rungumi yin noma ta hanyar fasaha..
Har ila yau, sanarwar ta yi kira ga daukacin manoman dake a kasar nan, musamman kananan manoma su rungumi yin aikin noma ta hanyar yin amfani da fasaha domin su bunkasa sana’ar su.
Sanarwar ta kara da cewa, idan aka yi la’akari da yadda rayuwar manoma na kasar nan da kuma wadanda suke a Afirka, inda kusan kashi 65 a cikin dari manoma ne, rungumar yin noma ta hanyar yin amfani da fasahar zamani ce kawai mafita a gare su.
A cewar sanarwar, mazaunan za a iya ba su horo na musamman kan sabbin hanyoyin fasahar ta aikin noma, domin su kara samar wa da kawunasu, kudaden shiga masu yawa.
Sanarwar ta kara da cewa, binciken kimiyya da sabbin abubuwa ciki har da ilimin kimiyyar kere-kere, za su taimaka wa manoman kasar matuka, musamman domin a kara samar da wadataccen abinci a kasar nan.
“Za a iya magance kmkalubale a fannin samar da abinci da rabar dashi a cikin sauki ta yayin hanyar fasahar kuma a halin yanzu, Afirka na iya samun damar ci gaba da fasaha ta zamani don magance kalubalen noma fiye da kowane lokaci na tarihi.”
A cewar sanarwa, wasu daga cikin wadannan kimiyoyin sun hada da nau’ikan amfanin gona mai bada amfanin gona wanda zai iya yin aiki sosai a cikin yanayin fari, zai iya tsayayya da kwari da cututtuka kuma suna iya amfani da abubuwan gina jiki sosa.
Sanarwar ta kara da cewa, sauran fasahohin sun hada da zabin sarrafa gona da kuma hanyoyin aikin gona na dijital don sarrafa amfanin gona da watsa ilimi, inda ta kara da cewa, duk da cewa nau’ikan samar da wadataccen abinci a kasashen duniya da dama.
Sanarwar ta kara da cewa, akwai hanyoyin da aikin gona na dijital da dama da ake yinnamfani da su wajen kara habaka amfanin gona kumanda su ne, kasashen duniya da suka ci gaba suke yin amfani don kara bunkasa nomansu.
Sanarwar ta ce, fasahar na kima kara taimaka wa wajen kara samun masu zuba jari a bangaren aikin noma, inda kuma sanarwar ta bayyana cewa, ya kamata Gwamnatocin kasar nan su horas da manoman dake a jihohinsu donbyin amfani da fasahar zamani wajen yin noma.

SendShareTweetShare
Previous Post

Karfafa Naira: CBN Zai Narka Dala Biliyan 15 A Matatar Dangote

Next Post

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kara Kaimi Don Farfado Da Ma’aikatun Ayyukan Noma

RelatedPosts

APPEALS

An Yaba Wa Yadda Nakasassu Suka Amfana Da Shirin Noma Na APPEALS   

by Muhammad
7 hours ago
0

Daga Abubakar Abba, Hukumar kula da masu bukata ta musamman...

Noman

Cibiyoyin Bincike Za Su Lalubo Hanyoyin Habaka Noman Dankalin Turawa Da Lemon Zaki A Nijeriya

by Muhammad
7 hours ago
0

Daga Abubakar Abba, Gwamnatin Tarayya ta umarci cibiyoyin binciken aikin...

Kaji

Murar Tsintsaye: Masu Kiwon Kaji Sun Tafka Asarar Fiye Da Naira Miliayan 500 

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Abubakar Abba, Sakamakon barkewar murar tsinyaye a Jihar Kano,...

Next Post
Gwamnatin Tarayya Za Ta Kara Kaimi Don Farfado Da Ma’aikatun Ayyukan Noma

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kara Kaimi Don Farfado Da Ma’aikatun Ayyukan Noma

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version