Noman Zoborodo Da Safararsa Zuwa Kasuwannin Duniya

Zoborodo

Daga Abubakar Abba,

Albarkar amfanin gona a Nijeriya na ci gaba da daga darajar kasar a matsayin kasar da a duniya ake mata kallon mai karfin tattalin arziki, musamman ganin cewa a Nijeriya ana noma dimbin amfanin gona da ake bukatar a wasu sassa da ke fadin duniyar nan.

A kasar nan, zoborodo na daya daga cikin kayan amfannin gona da ake nomawa, musamman ganin cewa, akwai dimbin masu son sayensa daga Nijeriya a kasuwannin duniya saboda yadda ake nomansa da dama a kasar nan.
Farasashinsa ga masu siya a kasuwannin duniya zai iya fara wa daga kashi 60 a cikin dari, zuwa sama da kashi  200, ya danganta idan kai manominsa ne ko kuma mai saye ne daga gona.
Ana sarrafa shu zuwa ganyen shaayi da kayan zaki da magungunan kiwon lafiya da sauransu, an kuma fi nomansa a Arewacin Nijeriya, haka an fi fitar da shi daga watan Okotoba zuwa na Maris.
Abin Da Yakamata Ka Sani Kan Fitar Da Ganyen Zobo Zuwa Kasuwar Duniya:
Nijeriya ta kasance ita ce, kan gaba wajen nomansa a nahiyar Afirka, inda kuma kasar Amurka da Jamani da  Holland da kuma sauran kasashen da ke nahiyar  Turai  da Asiya, suka kasance a kan gaba wajen shigar da shi zuwa kasashensu.

Damar Da Ake Samu Wajen Fitar Da Shi Kasuwannin Duniya:
1. Akasari farashinsa ya kan sha bamban a gona ko kuma a kasuwanin cikin gida, inda daga baya kuma a sayar wa da masu bukata a kasuwar duniya kan farashi daban-daban.
2. Idan ka kasance ba ka da kudi a hannunka don fara yin wani Kasuwancin,matakin farko kana iya zama a matsayin dan na-kama a wannann kalar kasuwancin wato, ka dinga hada mai saye da sayarwa, haka a fannin hada-hadar Zoborodo za ka iya yin hakan.

Yadda Za Ka Kafa Kasuwancin Fitar Da Zoborodo Zuwa Kasuwar Duniya:
1. Yi Wa Kasuwancin Rijista A Matsayin Kamfani:
Wannan shi ne matakin farko da za ka yi a gun hukumar yi wa sana’oi rijista ta kasa CAC, sai kuma a gun cibiyar NEPC.
2. Sayen Ganyen Kai Tsaye Daga Gona Don Fitarwa:
Mataki na biyu ka samu shi, kai-tsaye daga gona, musamman domin samun farashi na kai-tsaye domin bi ta hanyar ‘yan na-kama, bata lokaci ne.

  1. Fitar Da Ganyen Zoborodo Ka Zuwa Kasuwar Duniya:
    Za ka iya tallata shi ta intanet ko kuma ta hanyar kulla yarjejeniya da masu saye da ke kasuwar duniya.

kalubalen Da Ake Fuskanta Wajen Hada-Hadar Fitar Da Zoborodo
1. Rashin kwarewa wajen hada-hadar fitar da shi na janyo wa mai fitar da shi rashin sanin takamaiman farashi ko kari kan farashin da sauransu.
2. Jami’an Gwamnati na iya kamawa a lokacin da aka yo jigilarsa zuwa inda za a ajiye shi.
3. Masu sayen na jabu, na iya batawa wasu son fitar da shi lokaci wajen yin tambaye-tambayen karya.
4. Akasarin wadanda suke son su shiga cikin fannin, sun kasance ba su da isassun kudaden da za su fara sana’ar.
5. Samun bata lokaci saboda yawan doguwar tattaunawa a tsakanin mai saye da mai sayarwa, musamman wajen biyan kudi.
6. Yawan ‘yan damfara a fannin da suke fakewa cewa su masu sayen zoborodon ne, na kawo rashin yarda a zuciyar manomansa.

Exit mobile version