Abubakar Abba" />

NPA Ta Bai Wa Kamfanin Intels Wa’adin Sati Biyu Da Ya Biya Bashin Dalar Amurka Miliyan 48 Da Ake Binsa

Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta kasa (NPA) ta umarci kamfanin Intels na kasa da ya gaggauta biyan sauran kudi dalar Amurka miliyan 48 daake binsa bashi zuwa ga cikin asusun hadaka na (TSA) na hukumar a cikin sati biyu.

Manajin Darakatar hukumar ta (NPA)  Hadiza Usman ta bayar da wannan umarnin a hirar da ta yi da da kafar yada labarai ta  CNBC Africa a ranar Talatar data gabata. Hadiza Usman ta yi barazanar cewar, hukumar ta zata kaddamar da soke aikin da aka bai wa kamfanin na Intels, in har kamfanin bai biya bashin ba a tsakanin wa’adin da aka bashi ba.

A cewar Hadiza, “wani abu daya da muka ji a game da kamfanin shi ne, na yin buris da zuba kudin a cikin asusun na hadaka.”

Ta kara da cewa,“kamar yadda kuka sani ne, gwamnatin Nijeriya ta kirkiro da asusun na hadaka ne wanda dukkan kudin shiga da aka tara, ake bukatar a zuba su a cikin asusun.”

Tace, kamfanin na Intels ya karbi kudin shiga da sunan hukumar tashoshin jiragen ruwa na kasa, amma yaki and had refused yabi ka’idar ta asusun, inda yaci gaba da ajiye kudaden a ma’ajiyar sa.

Hadiza tace, “a saboda haka, na bai wa kamafanin na dama ta sati biyu da ya biya bashin, wanda daga nan za’a biyo da sanarwa ta soke shi, kuma sokewar, zata tsaya idan kamfanin ya gaza biyan bashin.”

Hadiza ta kara bayyana cewar, yanada mahimmanci kamfanin yabi ka’ida da aka shinfida wajen gudanar da ayyukansa.“

A cewar ta ‘Ina ganin yanada mahimmaci ga dukkan sauran masu gudanar da ayyukan su, suma su dinga bin ka’idar da aka shinfida.” Hadiza ta yi nuni da cewa,“ abida muke so mu tabbatar shi ne, kana da dama da aka baka kuma dole ne a cika ka’idojin da aka gindaya.”

Ta bayyana cewar, babu wani lokaci da hukumar ta bata zuba abinda ta tara ba, kuma dukkan sauran kashi na uku na yarjejeniya, da muka yi a hukumar mu, muna da tsare-tsare, amma mai ya sanya kamfanin na  Intels yake jin ba zai bi ka’idar da aka gindaya ba?

Tace, sauran kamfanonin duk suna bin ka’idojin da aka gindaya, me ya sanya ku baza ku bi ba.?

Kamfanin na da hukumar ta sun jima suna kai ruwa rana akan gudanar da ayyukan sa tun a watannin da suka gabata na shekarar 2017, inda hakanya sanya Ministan Shari’a kuma Atoni na kasa, Abubakar Malami, ya umarci hukumar data ajiye yarjejeniyar jiragen na data amince na

kamfanin, kuma ministan ya kara da cewar, yarjejeniyar, data bawa kamfanin na Intels dama ya karbi kudaden shigar a madadin hukumar ta ashekaru sha bakwai da suka shige, ta sabawa sasssana na 80 (1) daya a cikin baka  da sashi na 162 (1) a cikin baka da (10) a cikin baka na kundin tsarin mulkin kasar nan.

A wata sabuwa kuwa, Majalisar Wakilai ta kasa, ta umarci mahukuntan kamfanin a cikin awa ashirin da hudu, ya zuba bashin a cikin asusun na hadaka. Shugaban kwamitin Majalisar na wucin gadi na tabbatar da ana zuba kudin a cikin asusun na (TSA) Abubakar Danburam, ya bayar da umarnin a lokacin da kwamitin ya yi zaman sa a bainar jama’a na gudanar da bincike.

Danburam ya kuma umarci kamfanin na Intels da ya bayar da cikakkun bayanai akan bashin da gwamatin tarayya ke binsa a cikin awa ashirin da hudu, tare da yin barazanar yin amfani da karfin ikon kwamitin, idan kamfanin ya gaza cika sharuddan na gwamnatin tarayya akan asusun na hadaka.

A martanin da kamfanin na Intels ya bayar a shekarar data gabata, ya riki afuwa ga hukumar ta NPA da kuma neman ayi yarjejeniya don kara dankon kasuwanci ta fahimta tsaknin kamfanin da kuma hukumar.

 

Exit mobile version