NPA Ta Kaddamar Da Kananan Jiragen Ruwa Don Saukaka Zirga-zirga A Matatar Man Dangote
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NPA Ta Kaddamar Da Kananan Jiragen Ruwa Don Saukaka Zirga-zirga A Matatar Man Dangote

bySulaiman and Bello Hamza
1 year ago
NPA

Ministan Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, ya jagoranci bikin kaddamar da sabbin kananan jiragen ruwa guda biyu don karfafawa tare da saukaka zirga-zirga a tsakanin matatar man Dangote da tashar jiragen ruwa na Lekki. An sanya wa jiragen ruwan sunan MT IRAGBIJI da MT BAMA.

Ana sa ran jiragen za su taimaka wajen sintirin jami’an tsaro a tsakanin matatar man Dangote da tashar jiragen ruwa na Lekki.

  • Dangote Ya Soki Sabon Tsarin Gwamnatin Tinubu
  • Hukumar NPA Ta Samar Da Naira Biliyan 501 Ga Asusun Kasa A 2023 – Bello Koko

A jawabinsa, Ministan ya ce, an dauki matakin samar da jiragen ruwan ne don karfafa matsayin Nijeriya a cikin kasashen duniya masu hada-hadar da teku a yankin Afrika.

Ya ce, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tsayu wajen ganin an karfafa kaddarorin Nijeriya da ke cikin teku.

Tun da farko, a jawabinsa Shugaban Hukumar Tashoshin JIragen Ruwan Nijeriya NPA, Mohammed Bello Koko, ya ce, samar da jiragen ruwan daukaka matsayin Nijeriya a tsakanin kasashen yankin Afrika masu mu’amala da teku.

Ya kuma bayyana cewa, za a yi amfani da jiragen ruwa a tsakanin matatar mai na Dangote da kuma tashar jiragen ruwa na Lekki wannan a yanzu ta zama babbar fata ga Nijeriya wajen bunkasar tattalin arzikinta, musamman ganin tana gab da fara tace gangan mai 650,000 a rana.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa
Labarai

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Next Post
Rahotanni Biyu Sun Tabbatar Da Cewa Philippines Kasa Ce Dake Bata Muhallin Tekun Kudancin Kasar Sin

Rahotanni Biyu Sun Tabbatar Da Cewa Philippines Kasa Ce Dake Bata Muhallin Tekun Kudancin Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version