Connect with us

NAZARI

NSA Babagana Monguno: Babban Masanin Harkar Tsaro

Published

on

Sabon salon gyara da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta zo da shi yana da alaka ne da irin jajirtattun mutanen da ke zagaye da shi. Musamman ma Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Mohammed Babagana Monguno da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Ba tare da wata tantama ba, wadannan mutanen sun kai kololuwa a fannoninsu. A lokacin da Janar Monguno ya kasance masanin harkar tsaro shi kuma farfesa Gambari cikakken masanin diflomasiyya da tsarin tattalin arziki ne.
Dangane da Janar Monguno, babu makawa aikin tattara bayanan sirri shi ne muhimmi a gaban shugaban tsaro na kasa. Wannan shi ne wurin da gogewar NSA Monguno ta ke aiki. A matsayinsa na mutumin da ya dauki lokaci mai tsawo yana aiki kan harkar tattara bayanan sirri, tabbatar da tsaro ga Nijeriya a wurinsa karamin aiki ne. Kafin ya zama mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a shekarar 2015, harkar tsaron kasar a wargaje yake. Amma da zuwansaa, tuni labari ya canza. An karya lagon ‘yan ta’addan da ke cin karensu babu babbaka.
Sai dai, kamar yadda yake cike da damuwa dangane da sabon salon hare-haren ‘yan bindiga a Katsina, ziyarar da NSA Monguno ya kai jihar tare da ministoci, Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu; Darakta Janar na DSS, Yusuf Magaji Bichi da kuma Darakta Janar na NIA, Ahmed Rufai Abubakar; ziyara ce mai cike da alfanu. A ziyarar, Monguno ya ce: “Dole ne mu dawo da kwanciyar hankali da walwala a zuktan mutane, wanda kuma gwamnan Jihar Katsina ya bamu tabbacin hadin kai yadda ya kamata.”
Yanzu lokaci ne da za a hada karfi da karfe wurin tunkarar matsalar rashin tsaron Nijeriya. Wannan shawarar tana da alaka da matsayar gwamnaonin jihohin arewa 19 da ake da su, wadanda suka ce za a dauki mafarauta, ‘yan sintiri da ‘yan banga domin tattara bayanan sirri da aikin sintiri.
Shugaban kungiyar gwamnonin arewa, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya ce, tuni kungiyar gwamnonin ta kafa kwamiti domin a fara daukar mafarauta da ‘yan sintiri aiki.
Amma ni a nan na yarda da bayanin masana wadanda ke cewa wannan matakin duk da abin a yaba ne, amma ba zai magance matsalar tsaro kamar yadda NSA Monguno ya shirya tarban abin ba. Abin a nan shi ne, su mafarautan da ‘yan sintirin ba su samu horaswan da za su tinkari wadannan ‘yan bindiga ba, wanda a karshe za su fada tarko ne kawai.
Ana iya ganin sauyin da aka samu a harkar tattara bayanan sirri tun bayan da Janar Monguno ya shiga ofis. Wanda kuma an ga amfanin haka a dukkanin sassan Nijeriya.
Da irin wannan tawagar da ta hada da Janar Monguno da Farfesa Ibrahim Gambari, yanzu shugaban kasa yana cimma nasara a manufofinsa.  Rayuwa tana kyautatuwa ga ‘yan Nijeriya.
An ci galabar ‘yan ta’adda a dukkanin fadin Nijeriya, ta yadda an kwace duk wani yanki da a baya yake hannunsu. Idan ka kwatanta halin da ake ciki a yanzu da shekarar 2014 za ka ga bambancin mai yawa ne. A 2014 rayuwar al’umma ba a bakin komi take ba. A wancan lokacin kananan hukumomi 17 da ke Borno a hannun ‘yan Boko Haram suke. Har ma sun dora tutocinsu.
Wannan duk cikin aikin Monguno ne na tattara bayanan sirri ya kai ga kame manyan masu garkuwa da mutane irinsu Chukwudi Dumee Onuamadike da Hamisu Bala Wadume da dai sauransu.
Dole ne a jinjinawa NSA Monguno a wannan kokari nasa na fuskantar ‘yan ta’adda. Tarihi ya adana cewa Janar Monguno masani ne kuma jajirtaccen Janar din soja (mai ritaya). Ya kasance Shugaban Sashen Tattara Bayanan Sirri na Rundunar Soja daga shekarar Yulin 2009 zuwa Satumbar 2011. Haka nan kuma ya zama Kwamanda na ‘Guard Brigades’ daga shekarar 2007 zuwa 2009.
Monguno a matsayinsa na Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro daga 2015 zuwa yau, ya yi aiki tukuru wurin kwato kananan hukumomi daga hannun Boko Haram, tare da tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun tsira daga wannan masifa na ‘yan ta’addan Boko Haram. Ana iya bugun kirji a ce, Shugaba Buhari ya yi dace wurin zabo mai ba shi shawara kan harkokin tsaro.
A karkashin Janar Monguno, tsarin tattara bayanan sirri cike yake da ayyuka na musamman – irinsu tattarawa da bahasi, da kuma daukan matakai a sirrance. Karin wani batu shi ne dakile yiwuwar fitar bayanan sirri.
Dangane da Farfesa Gambari kuwa, mutum ne da ya san aiki, ya san diflomasiyya. Mutum ne da ya san cikin Nijeriya da kasashen waje. Fiye da kowa, Farfesa Gambari ya taimaka wurin kyautata mutuncin Nijeriya a idon duniya.
Wannan dama da Gambari ke da ita ta iya yin magana da kasashen duniya ba karamin abu ba ne. yanzu kuma da ya zama shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, za a amfana da kwarewarsa a mu’amala tsakanin Nijeriya da kasashen duniya.
A tsawon wadannan shekarun na Janar Moguno ya mayar da hankali wurin tattarawa, amsa da sarrafa bayanan sirri. A gabadaya rayuwarsa, Monguno yak an mayar da hankali matuka ga bayanai tare da kwarewa wurin bibiya.
A matsayin na shugaban tattara bayanan sirri na Nijeriya, Janar Monguno ya kware matuka wurin iya mu’amala da mutane. Dama kuma aiki ne da ke bukatar mutumin da ya iya mu’amala cikin natsuwa da sanin ya kamata.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

Advertisement

labarai