Muhammad Awwal Umar" />

NSCC Ta Yi Kira Na Musamman Ga Masauratun Jihar Neja

Asabar din makon nan masarautar Minna tayi bukin nadin Wakilin sarkin minna da Walin Minna karami, bukin dai ya samu halartar manyan mutane da dama har daga wajen jihar.

Da yake tsokaci akan bukin da masarautar ta shirya, shugaban kungiyar Niger State Concerns Citizen Alhaji Awaisu Wanna ( Wakilin Gwari-Nupe) a yammacin asabar din, yace gaskiya abinda masarautar minna tayi, tayi kuskure babba, domin jama’ar masarautar na cikin tashin hankalin mahara da ke kawo masu hare-hare a matsugunnan su wanda hakan ya sanya dukkan kusan mutanen karkara da suka fito daga yankin karamar hukumar Shiroro sun watse sun bar gidajensu wanda karamar hukumar Shiroron daga nan ne sarkin ya fito.

Ba mun ce bada sarautar kuskure ba ne, amma yin bukin a irin wannan halin da ake ciki shi yasa jama’a ke ganin kamar masarautar ba ta damu da halin da talakawan da ke cikin masarautar nan ba, idan ka duba irin kudaden da aka kashe a wannan bukin da an yi anfani da su wajen tallafawa mutanen nan da ke gudun hijira da jama’a sun yaba.

Zuwa yanzu Allah kadai yasan adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren maharan, da kuma irin hasarar miliyoyin kudaden da aka yi hasara da sunan Kudin fansa wanda maharan ke karba a hannun talakawa.

A kullun sai ka ga baki ‘yan gudun hijira sun watsu a cikin garuruwa ba tare da sun san inda suka nufa ba, amma har yanzu ba wani lokacin da masarautar minna ta ware dan nuna alhininta akan wadannan musifun da ke faruwa. Ya kamata mai martaba sarki, Dakta Umar Faruk Bahago a matsayinsa na uba kuma sarki mai daraja da ya dubi Allah ya bi duk hanyar da ta dace wajen lalubo hanyar da za a kawo karshen wannan lamarin a masarautar minna.

Ya kamata kamar yadda muka Shehun Barno yayi a lokacin da Boko Haram suka addabi al’ummar sa, na tashi zuwa fadar shugaban kasa da bin manyan jami’an tsaro wajen kawo dauki a masarautar sa wanda kowa shaida ne a kasar nan akan irin jajircewarsa na ganin talakawan Barno sun samu zaman lafiya, amma mu yau ga halin da muke ciki kusan dukkanin karkarun da ke kan iyaka da masarautar Rafi an watsa su kuma ba wani matakin tausayawa da ake nunawa jama’ar nan, gaskiya muna kalubalantar fada akan wannan sakacin da take yi kan maganar tsaro.

Abinda muke tsammanin duk wani rawani da masarauta za ta bayar, tana bada shi ne ga irin gudunmawar da mutum ya bayar na cigabanta, amma kusan yanzu sarautun sun zama ado, masu rawunna ba sa iya wakiltar al’umma illa su sanya babban riga da rawani a ce mai sarauta kaza amma idan ka duba sakamakon ayyukan da yayi ba wani gudunmawar da ya iya baiwa jama’ar da ke karkashin masarautar, yanzu me ye ribar wadannan kudaden da aka kashe wajen wannan bukin, babfa sarautar yanka ba ne, ba kuma wani anfani zai yi ba wajen tallafawa jama’a illa ga su makusantar sarkin.

Yaran da aka nada din, daya kani ne gare ni, dayan kuma dana ne amma abinda muke cewa tsaron rayukan jama’a da dukiyoyinsu shi ne mafi muhimmanci akan wannan bukin da aka kashe miliyoyin naira akan su, dan haka ina jawo hankalin mai martaba da ya tashi tsaye wajen ganin an samu zaman lafiya a masarautar minna, domin talakawa na da hakki akan shi na kare rayukansu da dukiyoyin su.

Muna bukatar masarautar minna tayi hubbasa wajen ganin an kawo karshen wadannan mahara dan mutanen karkara da suka dogara da noma da kiwo su koma gidajen su dan cigaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba.

Exit mobile version