Connect with us

LABARAI

NSCDC Sun Cafke Mai Jabun Dalar Amurka 3000 A Gombe

Published

on

Jami’an hukumar tsaron farin kaya Nigerian Security and cibil defence corps NSCDC a jihar Gombe sun kama wani Augustine Samuel da jabun dalar Amurka 3000 da adadin su suka kai naira miliyan daya da dubu tamanin a kudin Najeriya.
Augustine Samuel mai shekaru 47da haihuwa dan asalin Yola ne na jihar Adamawa.
Da yake gabatar da Wanda ake zargin wa manema labarai a helkwatar hukumar jami’an hulda da jama’a na hukumar a madadin Kwamandar Altine Sani Umar, ASC I Buhari Saad, yace sun samu baya nan sirri ne da ya taimaka musu wajen kama Wanda ake tuhumar.
Jami’an hulda da jama’ar yace sun kama Augustine Samuel,ne da jabun dalar Amurka na dala 100 guda 30 da kimar su a kasuwan canji ya kai naira miliya daya da dubu tamanin.
Buhari Saad, ya yi amfani da wannan samar ya godewa al’umma na yadda suke basu hadin kai wajen samun bayanai da suke taimaka musu suke gudanar da aikin su.
Yace wanda suke zargin an kamo shi ne a garin Yola na jihar Adamawa a ranar Talatar da ta gabata kuma ya amince da laifin da ake tuhumar sa akai.
Sannan yace sun kama shi ne ta hanyar jami’an su na sirri da zarar kuma sun kammala bincikensu za su tura shi zuwa kotu dan fuskatar Shari’a.
Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da basu hadin kai da goyon baya dan gudanar da aikin su.
Da wakilin mu yake zantawa da Augustine Samuel dan jin ko ya amince da tuhumar da ake masa sai yace shi daga Abuja ya taho da kudin ba shi yake bugawa ba kuma ya samu ne a gidan da yake gadin a can a Abuja din
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: