Hedkwatar Hukumar Tsaro ta Cibil Defence (NSCDC) ta Jihar Kano ta kama wani matashi da ake zargi da satar babur da kuma wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a Karamar Hukumar Kumbotso ta jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Abdullahi, ne ya tabbatar da kama wadanda ake zargin cikin wata sanarwa da aka ra wa jaridar The PUNCH a ranar Talata.
- Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya
- Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle
A cewarsa, “Jami’an hukumar NSCDC ta Jihar Kano, bisa sahihan bayanan sirri, sun kama mutum biyu, daya da ake zargi da satar babur a Sabuwar Jiddah, Yan Kusa, da kuma daya da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a Sabon Titin Dorayi dukkansu a Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.”
Ya ce wanda ake zargin mai satar babur din mai suna Usman Abdulhamid, mai shekara 19, mazaunin Yandanko, Panshekara, an kama shi jim kadan bayan ya sace babur a yankin Sabuwar Jiddah daga hannun wani da bai san da makircin ba.
Abdullahi ya kara da cewa yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin wata kungiya da ta kware wajen sata da kuma kwace babura a sassa daban-daban na birnin Kano.
Ya kara da cewa yayin gudanar da aikin, jami’an hukumar sun gano babura hudu daga hannun wanda ake zargi babura uku na Jincheng da daya na Lifan Kumata, inda ya ce ana ci gaba da neman sauran abokan aikinsa biyu da suka tsere.
Haka kuma, ya bayyana cewa an kama mai safarar miyagun kwayoyi mai suna Salisu Abdullahi, dan shekara 28, mazaunin Semegu a Karamar Hukumar Kumbotso, a yankin Sabon Titin Dorayi, tare da tarin miyagun kwayoyi da ake zargin yana sayarwa don amfani na haram.
Kwayoyin da aka samo daga hannunsa sun hada da kwayoyi 100 na Padol 5mg, kwayoyi 30 na Pregabalin 300mg, kwayoyi 170 na Diazepam 10mg, da kuma kwaya guda daya ta karin karfin maza.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan kamun na cikin dabarun hukumar wajen rushe kungiyoyin masu aikata laifuka da ke da hannu a satar kayayyaki, lalata dukiyoyin jama’a da sauran miyagun ayyuka da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.”
Abdullahi ya ce ana ci gaba da bincike a kan wadanda ake zargi, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala binciken.
A ranar 6 ga Nuwamba, jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa hukumar NSCDC ta Jihar Kwara ta kama mutane biyar bisa zargin satar igiyoyin wutar lantarki na transifoma da na fitilun titi a yankin Tanke da ke Ilorin.
Wadanda aka kama sun hada da Samson Akintola, Muhammed Zakariya, Mohammed Monsur, Ibrahim Hamida, da Kabir Abubakar.
An kama su ne da misalin karfe 1 na safe a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, yayin hadin gwiwar aikin jami’an NSCDC daga sashen Tanke Dibision da kuma Kungiyar Tsaro ta Bijilante ta al’ummar Tanke.














