An yi nasarar ceto wata mata wacce ’yan uwanta su ka kulle ta a wani daki tsawon wata biyar. Matar da aka ceto mai suna Saratu Ayuba tana zaune ne a unguwar Bolari da ke garin Gombe. An rufe matar ne bisa zarginta da ake yi da yin cikin shege tare da haifewa, inda rundunar tsaro ta NSCDC a Jihar Gombe ta ceto ta.
Matar mai shekaru 35 wacce ‘yan uwanta su ke zargi da yin cikin shege, sun kulle ta tsawon fiye da wata biyar. An ceto Saratu Ayuba da ke zama a kwatas din Bolari a birnin Gombe sakamakon wasu bayanai da aka samu daga makwabta, bayan sun gano halin da ta ke ciki na azabtarwa. Wasu yayyenta maza ne su ka rufe ta a daki tsawon sama da watanni biyar, bayan zargin cewa ta yi cikin shege da kuma haifewa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Shaidu sun bayyana cewa an daure Saratu da mari tare da jaririyar da ta haifa ‘yar watanni biyu a cikin wani daki mara tsafta, a gidansu da ke Bolari.
Saratu, wacce ta tsinci kanta a cikin wani yanayi mara kyan gani ba tare da suturar kirki ba, ta ce shayi da biredi kawai ake bata sau daya a rana tsawon watanni biyar da ta yi a kulle.
Ta ce tsohon mijin nata ya yi mata saki biyu bisa kuskure. Ta kara da cewa tana da ’ya’ya biyu a aurenta na farko; Alkasim mai shekaru 10 da kuma Fatima shekara takwas. Sai dai kuma, yayan Saratu mai suna Muhammad Tajuddin ya ce sun kulle ta ne bayan likitoci sun gano tana da tabin hankali.