Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

NSCIA Ta Soki CAN Bisa Zargin Nuna Wariya Kan Nadin Alkalan Kotun Daukaka Kara

Majalisar kolin Musuluncin Ta Fayyace kididdigar Nadin

by Sulaiman Ibrahim
March 31, 2021
in LABARAI
6 min read
NSCIA Ta Soki CAN Bisa Zargin Nuna Wariya Kan Nadin Alkalan Kotun Daukaka Kara
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya

Majalisar Kolin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) ta sanya kafa ta shure ihu da kumfar bakin da ta ce, kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ke yi kan batun jerin alkalai 13 daga cikin 20 da hukumar kula da harkokin shari’a a Nijeriya (FJSC) ta fitar na Kotun daukaka kara.
Majalisar Kolin ta kuma ce, idan har CAN za ta kwashe adadi sau biliyan daya tana kokarin danne Musulmi, ta sani ba za ta taba iya dishashewa ko danne hasken addinin Musulunci a wannan kasar ba.
Har-ila-yau, Majalisar NSCIA ta kuma ce, zargin neman musuluntar da sashin shari’a da CAN ta yi, abun kunya ne ma da kaito bisa la’akari da zahirin gaskiyar kididdigar yawan alkalan da suke cikin Kotun daukaka kara da sashen shari’a a halin yanzu wadanda Kiristoci sun ninka adadin Musulmai a tsakanin adadin alkalan kotun ta daukaka kara a Nijeriya.
A wani sanarwar da Farfesa Salisu Shehu, Mataimakin Babban Sakataren kungiyar NSCIA ya sanya wa hannu, tare da Farfesa Salisu Shehu, wamda shine Mataimakin Babban Sakataren Majalisar, da Arc. Haruna Zuberu Usman-Ugwu da kuma Daraktan Riko na Mulki na NSCIA din, sanarwar ta nuna cewa, kidaddiga ta nuna yadda Kiristoci suka fi mamaye guraben alkalanci a Nijeriya, wanda kukan da CAN ta yi, na nuni da kiyayya da gabar da take da su ga Musulmai ne kawai suka fito karara.
“Wannan na kara fitowa balo-balo yadda CAN ke nuna kyama da kiyayya ga Musulmai da addinn Musulunci ta haka ne suka dauki hanyar yada farfaganda domin cimma manufarsu wanda kuma sam hakan bai dace ba.”
kungiyar ta yi tilawar cewa, a wasu shekarun baya, CAN din ta taba yin wani zargi makamancin wannan wacce ta ce a gidan talabijin mallakin gwamnatin tarayya NTA ana nuna musu wariya da kiyayya wanda alatilas kungiyar ta fito ta warware zare da abawa domin CAN tana wawantar da hankalin al’umma.
Sannan, NSCIA ta nuna cewa ba za ta lamunci irin karerayin da CAN ke fitarwa domin tada hankalin jama’a da sunan addini ba, don haka ne ma ta nemi fito da hakikanin batutuwan da suke akwai domin jama’a su fahimta.
kungiyar ta ce, nadin Alkalai 13 daga cikin 20 da aka yi wa musulmai ba yana nufin an fifita wani addini a kan wani bane illa domin bin matakan aiki yadda suka dace, “Duk da cewa nadin Shugaban kotun daukaka kara, Monica Dongban-Mensem, da aka mata an yi nadin ne bisa tsarin da ke akwai ba tare da bin wani banbanci na kabila, addini ko yare ba. Amma ba musu sukar ba su soki nadinta ba (Kila don ita kirista ce). Duk kuwa da cewa CAN ta shure zahirin gaskiya na cewa musulmai sun fi yawa a kotun daukaka kara, amma kuma Kiristoci suka fi samun Alkalanci. A wani sanarwar kungiyar da take ikirarin kanta da ta addini ta nuna kyama son zuciya da nuna bacin rai kan jerin sunayen Alkalan da FJSC ta fitar.”
NSCIA ta ce, duk adalcin da ake yi amma CAN ta shure kafa ta ki dubawa sai fito da batutuwa marasa kan gado, “Zahirin gaskiya, Alkalan kotunan daukaka kara (JCSs) guda 70 ake da su a Nijeriya, Arewa da ke da jihohi 19 na da 34 a yayin da Kudu da ke da jihohi 17 ke da Alkalan kotunan daukaka kara 36. Hakan na nuna cewa Kudu ta fi Arewa yawan Kotunan daukaka kara.
“A halin da ake ciki, daga cikin Alkalan Kotun JCAs da ke Kudu Maso Yamma (Yankin da Musulmai ke da rinjaye), da Kudu Maso Gabas, da Kudu Maso Kudu, (Ba a tsaya alakari da musulmai ‘yan asalin yankunan ba), dukkanin Alkalan Kotunan Kiristoci ne ban da Justice Habeeb Adewale Abiru na Legas da kuma Justice Mistura Bolaji-Yusuf na jihar Oyo.
“Amma a shiyyoyi uku na Arewa wadanda dukka musulmai ke da rinjaye, daga cikin Alkalan Kotunan daukaka kara JCAs guda 34 da shiyyar da ke da su, Alkalai 15 Kiristoci ne,” kungiyar tana cewa, dukka da wadannan musulmai ko ‘yan Arewa babu wanda yayi korafin wariya sai CAN ce za ta bijiro da ikirarinta na rashin kan-gado.
Majalisar Kolin Musuluncin ta kuma fitar da kidaddiga da jerin sunaye da shiyyoyin da Alkalan suka fito wanda ke nuna balo-balo Kiristoci sun fi musulmai samun moriyar kujerun.
“A Arewa Maso Gabas Musulmai 4 ne kacal Alkalan kotunan JCAs sannan Kiristoci 7 ne; a Arewa Maso Tsakiya, Musulmai JCAs 6 ne a yayin da Kiristoci kuma 7 ne; a shiyyar Arewa Maso Yamma musulmai 9 ne Alkalan kotunan daukaka kara sai kuma Kirista guda daya. Amma gaba daya daga cikin Alkalan kotun daukaka kara guda 36 da ke shiyyar Kudu, Musulmai biyu ne kacal ina adalci a ciki wanda mu ba mu yi korafi ba sai CAN?”
Majalisar Kolin Addinin Musuluncin ta fitar da jerin sunayen Alkalan Kotunan daukaka kara da kuma shiyya da addinin kowani Alkali domin jama’a su gane wacce addini ke da mafi rinjaye.
Ta ce, Alkalan kotun daukaka kara da suke shiyyar Arewa maso tsakiya bakwai daga cikinsu Kiristoci ne a yayin da Musulmai su shida ne kawai.
“A shiyyar Arewa Maso tsakiya akwai Joseph S. Ikyegh Benue Kirista ne; Patricia A. Mahmoud Benue Kirista ne; Stephen Jonah Adah Kogi Kirista ne; S. T. Hussaini Kogi Musulmi ne; Ahmad O. Belgore Kwara Musulmi ne; M. N. Oniyangi Kwara Musulmi ne; F. A. Ojo Kwara Kirista ne.
Sauran Alkalan kotun daukaka kara a shiyyar Arewa maso tsakiya sun hada da “Ridwan M. Abdullahi Nasarawa Musulmi ne; J. Abungada Nasarawa Kirista ne;
Amina Wambai Niger Musulma ce; M. B. Idris Niger Musulmi ne; ita kanta shugabar kotun daukaka kara (PCA) Monica Dongban-Mensem daga jihar Filato; Kirista ce; Jummai H. Sankey Plateau Kirista ce.”
Sai kuma a shiyyar Arewa Maso Gabas da ake da Alkalan Kotunan daukaka kara Musulmai 3 Kacal Kiristoci kuma 8 duk da kasancewar shiyyar Musulmai ce.
Ga jerin sunayen da kungiyar ta fitar, “A. M. Talba Adamawa (Musulmi); Hussein Mukhtar Bauchi North East Muslim; Haruna S.Tsammani Bauchi North East Christian; Bitrus G.Sanga Bauchi North East Christian; A. G. Mshelia Borno North East Christian; Ibrahim S. Bdliya Borno (Kirista); Hamma Barka Gombe (Kirista); Y. B. Nimpar Gombe (Kirista).
Sauran Alkalan a shiyyar Arewa maso gabas su ne, “Mohammed Danjuma Taraba (Kirista); I. A. Andenyangtso Taraba (Kirista); sai kuma Mohammed Mustapha daga jihar Borno wanda ya kasance (Musulmi).”
Sai kuma shiyyar Arewa Maso Yamma kirista daya ne tak a yayin da Alkalan kotunan daukaka kara 9 duk musulmai ne, ga sunanesu da garuruwansu kamar haka:
“Ali Abubakar Gumel Jigawa (Musulmi); Muhammed L. Shuaibu Jigawa (Musulmi); Abubakar Dati Yahaya Kaduna (Musulmi); James S. Abiriyi Kaduna (Kirista); T. Y. Hassan Kano (Musulmi); A. M. Bayero Kano(Musulmi); Abubakar Sadik Umar Kebbi (Musulmi); Jamilu Y. Tukur Katsina (Musulmi); A. M. Lamido Sokoto (Musulmi); da kuma Alkali B. B. Aliyu Zamfara wanda ya kasance mabiyin addinin Musulunci ne shi.”
Sai kuma a jihohin Kudu, Kiristoci Alkalan Kotunan daukaka kara 16 Kiristoci ne, yayin da kuma 18 suka kasance Musulmai.
A shiyyar Kudu Maso Gabas dukkanin Alkalan kotuna 11 da ake da su, duk kiristoci ne ga su nan kamar haka: “Raphael C. Agbo Enugu Kudu Maso Gabas (Kirista); U.I Ndukwe- Anyanwu Anambra Kudu Maso Gabas (Kirista); Chidi N. Uwa Abia Kudu Maso Gabas (Kirista); C. E. Nwosu-Iheme Imo Kudu Maso Gabas (Kirista); T.N Orji-Abadua Imo Kudu Maso Gabas (Kirista); Obande F. Ogbuinya Ebonyi Kudu Maso Gabas (Kirista); Uchechukwu Onyemanam Ebonyi Kudu Maso Gabas (Kirista); Onyekachi A. Otisi Abia Kudu Maso Gabas (Kirista); C.I. Jombo-Ofo Abia Kudu Maso Gabas (Kirista); Paul O. Elechi Ebonyi Kudu Maso Gabas (Kirista) sai kuma Ugochukwu A. Ogakwu Enugu Kudu Maso Gabas (Kirista).”
Sai kuma shiyyar Kudu Maso Kudu wacce ke da Alkalan Kotunan daukaka kara 12 kuma dukkaninsu Kiristoci ne, babu musulmi ko daya, ga jerin Alkalan kamar haka: Ignatius I. Agube Cross daga jihar Riba (Kirista); Rita N. Pemi Delta (Kirista); Ita George Mbaba Akwa Ibom (Kirista); Moore A. A. Adumein Bayelsa (Kirista); O.O. Daniel-Kalio Ribas (Kirista); Fatima O. Akinbami Edo (Kirista); Biobele A. Georgewill Ribas (Kirista); Frederick O. Oho Delta.
“Sauran sune: Joseph E. Ekanem Akwa Ibom (Kirista); Abimbola O. Obaseki-Adejumo Edo (Kirista); Boloukuromo M. Ugo Bayelsa (Kirista); Ebiowei Tobi Delta (Kirista).”
A sanarwar da kungiyar ta fitar, ta nuna cewa a shiyyar Kudu Maso Yamma, Alkalan Kotun daukaka kara 11 Kiristoci ne, yayin da Musulmai guda biyu ne kawai, “Jimi O. Bada Osun (Kirista ne); Oyebisi F. Omoleye Ekiti (Kirista ne); Mojeed A. Owoade Oyo (Kirista ne); A. O. Lokolo-Sodipe Ogun (Kirista ne); Isaiah O. Akeju Ekiti (Kirista ne); Tunde O. Awotoye Osun (Kirista ne); Habeeb A. O. Abiru Lagos (Musulmi ne); Peter O. Ige Oyo (Kirista ne); O. A. Adefope-Okojie Ogun (Kirista ne); Mistura O. Bolaji- Oyo (Musulmi ne shi).
Sauran kuma dai sune, E. O. Williams-Dawudu Lagos (Kirista ne); Joseph O. Oyewole Osun (Kirista ne); Gabriel O. Kolawole Osun (Kirista ne).
A takaice, kungiyar ta ce, “A jihohin Kudu Kiristoci 34 ne Alkalan Kotunan daukaka kara, musulmai guda biyu tak. A jihohin Arewa ciki har da birnin tarayya Abuja, Kiristoci 16 ne Musulmai 18.”
“Adadin kiddidigar da ke akwai dukkanin Alkalan kotun daukaka kara (JCAs) kiristoci 70 na da kaso (71.4%), yayi da Musulmai kuma su 20 masu kaso (28.6%).
“A bisa wannan adadin da ake akwai, wacce addini ce aka danne ko ake wa wariya? Bai dace CAN take fito da karerayi ba, irin Kiristocin da suke cikin Kotun daukaka kara har CAN ta samu bakin yin zargin yunkurin Musuluntar da sashin shari’a? wannan abun kaito da Allah wadai ne.
“CAN dai ta sani ba zata taba iya danne hasken Musulunci a Nijeriya ba.”
kungiyar ta ce, da irin wannan dabara da hikimar ce kiristoci ke amfani da shi wajen kawo cikas ga batun sanya hijabi ga dalibai a jihar Kwara, duk da yake kungiyar ta ce Hijabi na daga cikin ababen da kundin tsarin kasa ya amince da su.
Majalisar Musuluncin ta tunatar da CAN cewa, akwai fa dokar kasa da ya bai wa kowane dan kasar dama da ikon gudanar da harkokin addininsa gwargwadon yadda ya fahimta ko ya ga dama ba tare da wata tsangwama ba.
Don haka NSCIA ta ce, batun haramta sanya hijabi da aka kawo a makarantun Jihar Kwara haramtacce ne kuma ya saba wa dokokin kasa, don haka ne ta soki CAN da matakan da take dauka na neman kara ruruta wutar rikicin da take kasar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Muna Addu’ar APC Ta Shekara 32 A Mulki – Sarkin Daura

Next Post

Ba Zan Kara Lamuntar Halin Da ’Yan Ta’adda Ke Jefa Talakawana Ba – Shugaba Buhari

RelatedPosts

Fasa Rumbunan Tallafi

‘Yan Daba Sun Tarwatsa Zaben Shugabannin PDP Na Shiyya

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa ’Yan daba sun tarwatsa taron Arewa...

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Gwamna Ganduje Ya Bukaci Kungiyar AFAN Da Su Kara Jajircewa Domin Habaka Tattalin Arziki

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi...

Yadda Aka Yi Bikin Nadin Galadiman Kazaure

Yadda Aka Yi Bikin Nadin Galadiman Kazaure

by Sulaiman Ibrahim
5 hours ago
0

Daga Ibrahim Muhammad Kano. A ranar Juma'ar da ta gabata...

Next Post
Minista

Ba Zan Kara Lamuntar Halin Da ’Yan Ta’adda Ke Jefa Talakawana Ba – Shugaba Buhari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version