Uwar kungiyar manema labarai ta kasa (NUJ) reshen jihar Yobe ta taya zababben gwamnan jihar- Mai Mala Buni, murnar samun nasarar zaben sa a matsayin sabon gwamnan jihar Yobe mai jiran gado, tare da shan alkashin goya wa gwamnatin sa baya domin kai jihar tudun mun tsira; da zaran an rantsar dashi, a ranar 29 ga watan Mayun 2019 mai zuwa.
Sakon taya murnar wanda yake kunshe a cikin takadar sakon da shugaban kungiyar, a jihar Yobe, Kwamared Yusuf Alhaji Isah ga zababben gwamnan, kana wadda aka raba ta ga yan jaridu a Damaturu, babban birnin jihar, a ranar Jumu’ar da ta gabata.
Yayin da ya bayyana cewa, zababben gwamnan, dama can mutum ne mai kyakkyawar alaka kuma abokin huldar yan jaridu a jihar; tun farkon shigar sa a fagen siyasa a jihar Yobe- kimanin shekaru 20 da suka gabata.
Ya ce “a matsayin mu na yan wannan kungiya ta manema labarai (NUJ), mun yi masa kyakkyawar shaidar halayen dattaku, wanda kowanne lokaci ba ya yin nesa da yan jaridu a dukan ayyukan sa. Wanda a kwana a tashi, Allah ya damka masa jagorancin al’ummar jihar Yobe baki daya, wanda a namu bangare zamu tallafa masa wajen samun nasarar yiwa jama’ar wannan jihar ayyukan ci gaba”. Ya bayyana.
Har wala yau kuma, Yusuf Isah ya yi amfani da wannan dama wajen yaba kokarin yan jaridu a jihar wajen bayar da ingantattun rahotani dangane da yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta gudanar manyan zabuka a cikin tsanaki da adalci.
Shugaban kungiyar manema labaran (NUJ) ya bayyana yadda a cikin shekaru 20 tsarin dimukuradiyya ya bunkasa a Nijeriya tare da zaburar da shugabanin da suka yi nasarar dare kujerun da suka yi takara da cewa su tuna girman Allah; su cika alkawuran da suka dauka wa talakawa, a lokutan yakin neman zabe.