Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Bauchi (NUJ) ta gabatar wa mambobinta da rahoton aikace-aikacen da ta gudanar a tsawon watanni bakwai da suka yi kan shugabancin. Inda suka gabatar da rahoton aikace-aikacensu daga ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa 30 ga watan Agustan 2017. Taron baje kolin ayyukan na kungiyar wanda ya gudana a babban dakin taro na NUJ da ke Bauchi, a shekaran jiya alhamis.
LEADERSHIP A Yau, Asabar ta rawaito cewar a yayin taron kungiyar ta gabatar wa mambobinta adadin kudaden da suka shigo wa uwar kungiyar tsakanin watanni bakwai 7 da kuma hanyoyin da aka samu kudaden. A cikin rahoton da ma’ajin kungiyar Abubakar Waziri da Sakataren Kudi Najib Sani da kuma Danjuma Sarki Sale Audito suka gabatar, sun bayyana cewar NUJ reshen Bauchi ta samu zunzurutun kudi naira miliyan daya da dubu dari hudu da hamsin da dari daya da bakwai 1,450,107.55 a tsawon watanninsu bakwai a bisa shugabacin kungiyar.
A rahoton nasu, sun bayyana cewar sun samu wadannan kudaden shigan ne ta hanyoyi irin su kason da kungiyar take samu a lokacin da ake taron manema labaru (Press Conferences), rahoton ya ce inda suka fi samun kudin shiga shi ne harajin kungiyoyin da suke karkashin uwar kungiyar ta NUJ wato (chapel-chapel) na watanni shida, sai kuma kudin taron manema labaru na ma’aikatar sadarwa ta jihar Bauchi na 2017, wanda jimillar kudin ya kai adadin da muka nakalto a sama.
Haka kuma rahotonsu ya nuna sun kashe wasu kudaden ta hanyoyin da suka dace. Sai kuma rahoton sashin kudi na NUJ suka ce yanzu abun da ya yi saura na daga kudi shi ne naira dubu 354,000. Sashin kudin, sun ce lokacin da suka amshi shugabancin NUJ bayan da aka gabatar da zabe a watan Fabrairu sun samu asusun ajiya na kungiyar da naira dubu 6 ne kacal.
Wakilinmu da ya kasance a cikin taron ya shaida mana cewa a yayin taron na “Congress” an tattauna kan abubuwan da suka shafi kungiyar da mambobinta, kana an kuma tattauna kan jihar ta Bauci da sauran muhimman abubuwa da suke faruwa a kasa. Haka kuma mambobin sun yi ta jero tambayoyi ga uwar kungiyar inda shugaban NUJ ya yi ta amsa wa mambobin tambayoyinsu da kuma koke-koken da suka gabatar wa uwar kungiyar ta jiha.
Baya ga nan, sauran ofis-ofis na kungiyar sun gabatar da rahoton aikace-aikacen da suka gudanar a yayin shugabancinsu na wata bakwai a matsayin su na shugabanin ‘yan jaridar jihar ta Bauchi.
A hirarsa da manema labaru jim kadan bayan kammala taron, shugaban kungiyar ‘yan jarida na jihar Bauchi Malam Ibrahim Malam Goje ya ce, “a bisa al’ada ana gudanar wannan taron ne a dukkanin bayan wata uku-uku domin fayyace wa mambobin kungiyar halin da ake ciki da kuma yi musu bayani kan aikace-aikacen da suka guda “taron yakan yi baya irin ziyarce-ziyarce da aka yi a cikin watanni uku, da aikace-aikacen da aka gudanar. A bisa haka ne muka yi wannan taron. Sannan taron ya gaji yin bayani kan nasarori da aka samu da kuma shirye-shiryen da ake son cimmawa a gaba. Haka kuma da tattaunawa kan inganta aikin jarida da jin dadin su mambobinmu”.
Kwamared Ibrahim Goje ya ci gaba da cewa “mun kuma gabatar da rahoton kudaden da suka shigo mana da inda aka kashe su, da kuma sauran abun da su ke asusun kungiyar”.
Shugaban na NUJ ya ce baya ga wannan sun kuma tattauna kan ci gaban jihar Bauchi ta yadda ‘yan jarida za su bi wajen taimaka wa jihar da al’umman jihar, uwa-uba da ci gaban kasar Nijeriya baki daya.
Ya ce, “bayan nan mun kuma fitar da sanarwar bayan taro wadda ta shafi ‘yan jaridanmu, jihar Bauchi da kuma kasa baki daya. Mun tattauna kan muhimman abubuwa da suka shafi mu suka kuma shafi al’umma”. In ji shugaban.
Wakilinmu da ya ji ra’ayoyin mambobin NUJ na jihar jim kadan bayan kammala zaman taron sun nuna gamsuwarsu da yadda shugabanin ke tafiyar da harkokin kungiyar na yau da gobe da kuma yadda suke sarrafa kudaden da suka shigo musu.
Daya daga cikin ‘yan jaridar jihar ya ce, “sun samu asusun kungiyar NUJ ta jiha da naira dubu shida ne kacal, a karin farko suka yi karo-karo daga aljihunsu inda suka samar da naira dubu 30 domin gudanar da aikace-aikacen kungiyar, ka ga wannan abun a yaba musu ne, ba su tsaya da aikin suka ce bari su jira sai kudade sun shigo kafin su yi wa mambobinsu hidima ba. Muna jinjina musu”.
Wasu ‘yan jaridan a wajen taron sun jinjina wa sabbin shuwagabanin kungiyar ‘yan jarida a bisa bada horo kan na’ura mai kwakwalwa da suka yi da hadin guiwar ATAP, kana an jinjina kan wasu aikace-aikacen nasu. Su dai shugabannin da suke mulkar ‘yan jaridan an rantsar da su ne a watan Fabrairun 2017, bayan gudanar da tsaftaccecciyar zabe a tsakanin mambobin ‘yan jarida a jihar.
Wannan taron dai shi ne karo na farko da suka yi tun bayan darewarsu kan karagar mulkin shugabantar ‘yan jaridan.
Wakilinmu ya rawaito cewar a sanarwar bayan taro, ‘yan jarida sun sha alwashin bada goyon baya domin kwantar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’a. Sun kuma bayyana cewa ‘yan jarida za su yi aiki da kwarewa wajen shawo kan matsalolin da suke faruwa musamman na masu fafatukar kafa ‘yankin Biyafa watau IPOB, da sauran tashi tashina da ake fama da su a kasar nan.
NUJ ta gabatar wa mambobin da suka halarci taron kasaitacciyar walima a wajen taron.
Taron wanda ya hada bangarorin ‘yan jarida suke fadin jihar Bauchi, da kuma wakilai daga kowace chapel na chapel guda 10 da suke karkashin uwar kungiyar na jihar Bauchi. Haka kuma an gudanar da taron ba tare da wata hanayi ko jani-in-jaka ba.