Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Sakkwato ta yaba da yadda aikin gina Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Jihar Sakkwato (SSUTH) da Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Mata ke gudana ba tare da tsaiko ba.
Kungiyar ta ce ayyukan biyu muhimmai wadanda idan aka kammala za su bayar da gagarumar gudunmuwa ga ci-gaban sha’anin kiyon lafiya, samar da kwararrun likitoci da samar da ayyukan yi a Sakkwato.
Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamred Isa Abubakar Shuni ne ya bayyana hakan a yayin da ya sake jagorantar manbobin kungiyar ziyarar duba ayyukan biyu da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayar da kwangila a Kasarawa. LEADERSHIP A YAU ta labarto cewar a watan Oktoba, kungiyar ta kai irin wannan ziyarar a karon farko domin gani da ido kan yadda ayyukan ke gudana, a yanzu kuma ta sake zagayawa.
Gwamnatin Tambuwal ta bayar da kwangilar gina Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Jihar Sakkwato a kan tsabar kudi naira biliyan 6.8 ga kamfanin Calder Construction tare da lokacin kammalawa a cikin watanni 30. Haka ma ta bayar da kwangilar gina Sakandiren Kimiyya ta Mata a kan kudi naira biliyan 2.4 ga kamfanin na Calder da watanni 18 na kammalawa.
“Mun gamsu da kwakkwaran aikin da dan kwangila ke aiwatarwa, kayan aiki da zubin aikin duka ingantacce ne. Muna fatar yadda suka fara aiki da farko yadda ya kamata da yadda suke a yanzu za su dore da haka ba tare da gudanar da aikin baban giwa ba. Aikin abin yabawa ne wanda muna da tabbacin zai kara bunkasa tattalin arzikin Jiha domin ma’aikatan da ke aikin duka ‘yan jiha ne haka ma a cikin Jiha ake sayen kayan mafi yawan kayan aiki.” In ji Shuni.
Tun da farko babban Injiniyan kula da aikin, Kabiru Umar Yabo ya bayyanawa manema labarai cewar aikin gina Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Jihar Sakkwato a na yin sa ne kan hekta 44 tare da cewar za su kammala a cikin lokaci.
Ya ce a yanzu haka aikin ya kai kashi 30 na kammalawa tare da cewar ma’aikata 1, 000 da ke aiwatar da aikin ‘yan Jihar Sakkwato ne. Haka ma ya ce a kan siyo kayan aikin a cikin jiha da makwabtan Jihohin Zamfara da Kabi. A cewarsa asibitin mai daukar gado 950 na da rukuni shida na sassan da ke daukar gadaje 96, sashen manyan mutane da manya-manyan mutane, tituna da sashen mulki da sauran su.
Kakkarfar tawagar ta ‘yan jarida, wadda kuma ta ziyarci makarantar Kimiya ta Mata a Kasarawa sun tarar aikin ya kai kashi 30 cikin 100 na kammalawa kamar yadda Manajin Darakta na kamfanin Kabiru Muhammad Sarki ya bayyana.
Ya ce makarantar ta kwanan dalibai ta na da ajujuwa 36, dakunan gwaje- gwaje hudu, dakin karatu na mai dauke da fasahar zamani, sashen mulki, gidajen malamai da dakunan kwanan dalibai