Shugaban kunkiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar kano, kwamred Abbas Ibrahim ya bayyana cewa, kunkiyar ‘yan jarida (NUJ) reshen kano na shawartar hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar kano karkashin jagorancin Farfesa Garba Ibrahim Sheka da ta dauki dukkanin matakai wajen ganin an gabatar da zaben kananan hukumomin kano 44 cikin kwanciyar hankali da lumana domin kaucewa duk wani abu da ka iya kawo barazana a tsakanin al`umma ta hanyar saitawa da fadakar da ‘yan siyasa muhimancin yin zabe cikin lumana da zaman lafiya.
Malam Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne a lokacin da NUJ ta gabatar da taron ta a harabar kunkiyar da ke birnin kano a makon da ta gabata. Haka zalika kuma ya yi amfani da wannan damar wajen jan hankalin al`umma wajen lura da yanayin sanyin huntoro da aka shiga domin kula da lafiyar kananan yara da kuma daukar matakai na ganin an yi amfani da wuta bai kawo matsala a wannan lokaci ba.