Daga Abubakar Abdullahi, Lafia
Ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa reshen Jihar Nasarawa ta yi yabo ga gwamnan Jihar, Umaru Tanko Al-Makura kan naɗa ‘ya’yanta uku a muƙamai daban-daban na gwamnatin jihar.
Shugaban ƙungiyar Mista Dogo Shammah ne yayi wannan yabon cikin wata sanarwa da ya miƙawa manema labarai a lafia fadar gwamnatin jihar.
Shammah ya bayyana jerin sunayen waɗanda gwamnan ya naɗa a muƙaman da suka haɗa da, Musa Elayo a matsayin sakatarensa na yaɗa labarai, Yahuza Idris a matsayin shugaban kwamitin riƙo na karamar hukumar lafia da kuma Mohammed Alhassan a matsayin mamba na kwamitin riƙo na karamar hukumar Karu.
Shugaban ƙungiyar ‘yanjaridu ya bayyana gwamna Al-Makura a matsayin uba ga aikin jarida a jihar.
Shugaban ‘yanjaridun ya kuma yi kira ga waɗanda aka naɗa a muƙaman da su bai wa maraɗa kunya ta hanyar yin aiki bilhaƙƙi da gaskiya domin ɗaukaka sunan ɓangaren da suka fito; wato fannin aikin jarida.
Kafin naɗin ‘yan jaridu uku a sabbin muƙaman wato Elayo, Yahuza da Alhassan sun kasance ne suna ayyuka a gidan rediyo da talabijin mallakar gwamnatin jihar da ma’aikatan yada labarai na jihar da kuma russasshiyar kamfanin buga jarida ta jihar.