Connect with us

LABARAI

NURTW Ta Wayar Da Kan Shugabannin Shiyyarta A Kan Illar Korona 

Published

on

An yi kira ga direbobi da su bi dokokin hukumar lafiya na kare kai kan annobar Koronabairus, shugaban kungiyar NURTW ta kasa reshen jihar Neja, Kwamred Garba Bala Musa ne yayi kiran a lokacin da yake jagorantar taron wayar da kan shugabanni shiyya da sakatarorin kungiyar na yankin Neja ta kudu ( Zone B) da kungiyar ta shirya a sakatariyarta da ke larabar makon nan.

Kwamred Bala ya jawo hankalin direbobi da su kaucewa shiga cinkoso kamar yadda hukumar lafiya ta bada shawara, haka ya zama wajibi duk direban da ke karkashin wannan kungiyar ya rika anfani da takunkumin fuska, haka kowani direba ya tabbatar bai dauki fasinjan da bai da takunkumin fuska ba domin idan jami’an kwamitin yaki da annobar Korona suka kama mutum ba ruwan kungiya, saboda haka wajibi ne kowani direba da fasinja su tabbatar sun sanya takunkumin fuska domin tsare lafiyarsu da rayuwa.
Kwamred Garba Bala ya ce kwamitin kula da annobar Korona ta jiha ta umurci dukkanin tashoshin mota da su samar da sinadaran wanke hannu da za a ajiye a kowace kofar shiga gareji da fita dan baiwa jama’a damar tsaftace hannayen su.
kungiyar ta umurci a rage yawan cinkoso a cikin tashoshi da motocin daukar fasinja, kowani shugaban shiyya ya koma ya zauna da ‘yayan kungiya a tattauna hanyoyin yadda za a bi kan farashin kudin mota kuma a tabbatar ba a takurawa kai ba musamman fasinja domin kowa yasan halin da ake ciki kuma a tabbatar an yi la’akari da mawuyacin halin da jama’a ke ciki ta yadda za mu cigaba da tafiya har Allah ya kawo mana karshen wannan halin da mu ke ciki. Idan gwamnati ta rage kudin mai, ba a rage kudin kayan gyaran mota ba.
Shugaban yace maganar safara daga wata jihar zuwa wata, har yanzu ba a amince ba, domin kamar yadda gwamnatin tarayya ta shelanta kowa ya tsaya cikin jihar sa, dan killace jihar daga yaduwar wannan annobar ta Korona.
“Direbobi ‘yan uwana su bada hadin kai, ya zama tilas mu da hadin kai a wannan yanayin da ake ciki, ba tallafin gwamnati za mu tsaya jira ba domin ita kan ta ba ta da kudaden da za ta gudanar da wannan famar da ake yi da wannan annobar,” in ji shi
Kwamred Garba, ya jawo hankali gwamnati akan abubuwa uku, matsalar tsaro, annobar Korona da gyaran hanyoyi, inda ya kara da cewa, “tana kokari amma dai ta kara kashe kashen da ake yi a kasar nan ya yi yawa, ana kashe mu kuma ana kashe ‘yan uwan mu ga matsaloli kuma na ta kara yawa”.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: