Abdulrazaq Yahuza Jere" />

NYSC Ta Karrama Dan Bautar Kasa James Shalom Fredrick

Shugaban Hukumar Kula da Matasa ‘Yan Bautar Kasa (NYSC), Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim mai ritaya ya karrama wani matashi da ya kammala aikinsa na bautar kasa, Mista James Shalom Fredrick bisa nuna kwazon aiki da taimakon jama’a ta hanyar ba da gudunmawar wata na’urar auna yanayin zafin jiki ga sakatariyar hukumar bautar kasa ta Abuja.

Shugaban hukumar wanda Babbar Jami’ar Kula da ‘Yan Bautar Kasa ta Abuja, Malama Walida Siddique ta wakilta, ya jinjina wa James Shalom bisa yadda aka yi amfani da na’urar da ya bayar wajen tantance yanayin zafin jikin mutane masu shiga sakatariyar hukumar lokacin da ake yaye matasa ‘yan bautar kasa rukuni na biyu na shekarar 2019.

NYSC ta mika wa James takardar yabo saboda nuna kishin kasa, kasancewar na’urar da ya bayar da gudunmawarta za ta taimaka wa ‘yan bautar kasa wajen yaki da cutar Korona wacce a sababinta aka soke faretin yaye matasa ‘yan bautar kasa kamar yadda aka saba tare da bin sharuddan da Hukumar NCDC ta shimfida na taruwar jama’a.

A jawabin da Malama Walida Siddique Isa ta yi, ta bayyana cewa, “James, ka nuna sadaukarwa da ladabi a lokacin da kake aikinka na bautar kasa. A sakamakon haka, ka fayyace nagartarka ga wadanda suka dauke ka aikin bautar kasa, da masu masaukinka da ma dukkan al’ummar Abuja”.

James Shalom wanda da ne ga jami’in yada labarun Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), DCI Sunday James, ya yi digirinsa ne a fannin nazarin ‘Physics’ a Jami’ar Landmark da ke Omu-Aran ta Jihar Kwara, kana ya yi aikinsa na bautar kasa a Hukumar Kula da Tauraron Dan Adam ta Nijeriya, shiyyar Abuja.

Exit mobile version