Connect with us

KASASHEN WAJE

Obama Ya Yi Kira Ga Matasa Su Fito Zabe

Published

on

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama, wanda ba a cika jin duriyar tun da ya bar mulki ya shiga rudanin zabe da aka yi a jiya jumma’a inda yace “ya kamata mutane suyi zabe, domin ‘yancin su ya ta’allaka a kan yin hakan”.
Ya ce, kaucewa yin hakan zai iya zama babban hatsari a garesu baki daya.
Tsohon shugaban na Amurka dai ya yi magana ne a lokacin da yake wa dalibai a jami’ar jihar Illions dake Urbana, jawabi inda ya karbi lambar yabo ta kwazo da akida a aikin gwamnati.
Obama ya kara da cewa halin da siyasar Amurka ke ciki yanzu, ba wai ya fara a zamanin Donalad Trump bane, amma yana daya daga cikin alamomi da ya ce, sun matsalolin da ‘yan siyasa suka fara haifarwa a shekarun baya ne.
Advertisement

labarai