Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Obasanjo: Ƙuliƙuli Wa Ya San Gabanka?

by
5 years ago
in BULALIYA
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

 Al-Amin Ciroma 08033225331 (TES Kawai )   ciroma14@yahoo.com       

Kwanan nan Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce har abada ba zai ƙara komawa PDP ba, a lokacin da na ji wannan zance nasa dariya ya kama ni, domin Obasanjo na ɗaya daga cikin waɗanda suka lalata harkar siyasar Nijeriya, musamman idan aka yi la’akari da rawar da ya taka kafin da bayan zaɓen 2015.

Idan muka waiwaya baya kaɗan a lokacin da ya samu damar ɗarewar mulkin ƙasar nan, ba a jima ba shi da mataimakinsa Atiku Abubakar suka fara samun takun saƙa a tsakaninsu. Obasanjo  shi ne shugaba na farko a jerin waɗanda suka mulki Nijeriya da ya fara fitowa bainar jama’a yana husuma da mataimakinsa. Koda yake dukkaninsu biyun mutane ne masu bankaura da zafin rai a fagen siyasa, waɗanda za ka ma iya fassara su da marasa haƙuri. Domin ko a lokacin, Atiku ya taɓa fitowa yana kuri yana hure hancin wai zai mari wani alƙalin kotu, saboda rashin jin daɗin hukuncin da alƙalin ya yanke na shari’ar zaɓen gwamna a jiharsa ta Adamawa.

Labarai Masu Nasaba

MUKALAR LITININ: Guguwar ’Yan A Kwafe – A Watsa A Yanar Gizo ‘Copy and Paste’

Tunaninka Kamaninka: Yaushe Za Ka Zama Attajiri?

Shi kuwa uban gayyar wato Obasanjo, salon siyasarsa daban ce haka ma bankaurarsa da rashin haƙuri duk sun shahara. Abubuwan ban mamaki da ya tafka a gidan gwamnati ba sa lissafuwa. Idan aka yi la’akari da waɗannan mutane biyu, irin yadda suka ɗauki tsawon shekaru takwas a mulkin Nijeriya, haƙiƙa babu wani wanda zai ɗauki zancen Obasanjo da mahimmanci.

Misalan na nan da dama, musamman ma yadda Obasanjon da Atikun suka haɗa kai, suka yi tafka aringizon ƙuri’u a zaɓukan shekarar 2003, da irin rawar da tsohon shugaban ya taka wajen ɗora Marigayi Umar Musa ‘Yar’Adua a bisa karagar mulki, don ya share wa Goodluck Jonathan hanyar shiga Aso Rock, sannan da yadda ya nuna gajen haƙurinsa a lokacin da Jonathan ya juya masa baya, har suka yi wa juna tonon silili cikin wasiƙun da duk duniya ta karanta. Haka kuma da jirwayen da ya yi mai kama da wanka, ya koma jam’iyyar APC saboda ya fahimci idan ya yi sake asirinsa zai tuno don kuwa jam’iyyar za ta iya yin nasara a zaɓukan, ya fake da cewar yana goyon bayan Muhammadu Buhari.

To, dukkanin waɗannan alamu ne da ke bayyana haƙiƙanin Obasanjo, wato mutum ne da ba shi da alƙibla kwatakwata a harkarsa ta siyasa da mu’amala. Za ma ka iya fassara shi da mutum ne mai fuska dubu, abin da Hausawa ke kira Ƙuliƙuli wa ya san gabanka?

Ya kamata manyan ‘yan siyasar Nijeriya su yi wa wannan tsohon taron dangi, su fitar da shi daga harkar siyasarsu, sannan su yi masa iyaka da shiga sharon da yake yi a harkar mulkin Nijeriya. Da a ce Obasanjo mutum ne mai nufin yi wa dimokuraɗiyyar Nijeriya adalci, kamar yadda yake yekuwa a yanzu, to sai mu tambaye shi; Me ya sa bai ɗauki ƙwararan matakai a kan badaƙalar da aka riƙa tafkawa a Jihar Anambara tsakanin Sanata Emmanuel Andy Uba, Sanata Chris Nwabueze Ngige da kuma Chris Uba ba? Abubuwa su na nan birjik babu isasshen shafin da za mu bayyana su.  Yana bisa gadon mulki ne  waɗannan ‘yan siyasar suka zauna a gabansa suka fallasa juna yadda suka tafka almundahana, babakere da aringizon ƙuri’u a lokacin zaɓukan da aka yi a Jihar Anambara, amma ko a jikinsa! Maimakon ya taka mu us birki, sannan ya bayar da umarnin a ɗauki mataki a kansu, sai ya kawar da kai, ya ci gaba da goyon bayan wanda ya ke ƙauna a tsakaninsu.

Irin wannan hali na Obasanjo shi ne ya haifar wa yankin Arewa da Nijeriya da kuma al’ummarta baki ɗaya halin da muka tsinci kanmu a ciki a yau. Ko a sa’ilin da suke mulkin Nijeriya, wanda a lokacin ne ƙasar ta samu bunƙasar tattalin arziƙi fiye da sauran lokuta a tarihi, amma abin takaici Obasanjo da Atiku suka yi haɗin gwuiwa wajen daƙile siyasar aƙida a Nijeriya, suka ci nasara cusa kuɗi a harkar siyasa, ba don komai ba sai domin biyan buƙatun kansu da kansu!

A halin gaskiya al’adar siyasar Nijeriya, musamman ma nan Arewa, jama’a na tsananin buƙatar ɗan siyasa ya kasance mutumin ƙwarai mai riƙon amana, wanda bai damu da son rai ba illa yi wa jama’a hidima daidai yadda doka ta shimfiɗa. Amma Obasanjo ya tirsasa wa Atiku wasa da ƙwaƙwalwar jama’a da kuɗi don cimma burorin kansu. Saboda haka ne tsohon shugaban ya riƙa zawarcin wasu daga cikin manyan ‘yan boko da na siyasar Arewa su shimfiɗa masa hanya ɗoɗar, wacce zai bi don ya gaji kansa da kansa da sunan tazarce a karo na uku, amma da aka bankaɗo shi, sai ya koma ta bayan fagge ya shirya maguɗin zaɓen da ba a taɓa yin irin sa a tarihin siyasun duniya ba, inda ya ci nasarar ɗora wanda ya so ya gaje shi.

Abin da Obasanjo bai sani ba shi ne, za a iya cusa wa ɗan Arewa kuɗi don yin wata harka, amma babu kuɗin da za ka ba wa ɗan Arewa da ya san mutuncin kansa don ka saye shi a siyasance! Mu dubi manyan mutane da suka fito daga yankin waɗanda suka riga mu gidan gaskiya irin su Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa, Sir Ahmadu Bello, Sir Kashim Ibrahim, Malam Aminu Kano da irin su Mista Joseph Tarka. Sannan mu kalli rayuwar waɗanda ke raye a yanzu kamar Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Muhammadu Goni, Malam Balarabe Musa da sauransu, dukkaninsu mutane ne da suka koyar da al’umma hanyoyin gaskiya da riƙon amana a siyasar aƙida. Kowannensu ya samar wa kansa manyan ɗabi’un girmamawar zai iya shiga kowane lungu da saƙo na duniyar nan, ba tare da jin tsoron komai ba.

Abin kunya da takaici, an wayi gari yau wai su Obasanjo ne iyayen ‘yan siyasar Nijeriya! Me za a tsinana? Abin takaici a zamaninsa ne aka samar da wasu gwamnoni masu ban mamaki a harkar mulkinsu. Joshua Dariye na Jihar Filato, alal misali, yana daga cikin gwamnonin da suka bayyana halin Obasanjo a salon mulkinsu. An samu matsaloli da dama a cikin gwamnonin lokacin irin Attahiru Bafarawa na Jihar Sokota da makwabcinsa Ahmed Sani (Yariman Bakura) na Zamfara da sauransu.

Ta’asar da Obasanjo ya shuka a Nijeriya ya zo daidai kuma ya na da kamanceceniya da irin wadda Hastings Kamuzu Banda, wato tsohon shugaban ƙasar Malawi ya tafka a ƙasarsa. Kamuzu ya shafe shekaru 33 yana cin karensa babu babbaka a kan karagar mulkin ƙasar Malawi kafin Bakili Muluzi ya gaje shi.

Sai da Kamuzu Banda ya kassara ƙasar baki ɗayanta, ya ci nasarar lalata harkar shugabanci, ya karya tattalin arziƙin ƙasa, satar dukiyar al’umma ta zama abin tinƙaho a tsakanin al’ummar ƙasar, kana kuma kuɗi ya riƙa jagorantar harkokin siyasa a Malawi. Da barinsa mulki yau shekaru 23, amma abin takaici har yanzu Malawi ba ta farfaɗo daga doguwar sumar da Kamuzu Banda ya haddasa mata ba, kamar yadda har yanzu Nijeriya ba ta farfaɗo da sharrin Obasanjo na shekaru goman baya ba.

Don haka lokaci ya yi a Nijeriya da al’umma za su ɗauki darussa da dama na abubuwan da ke faruwa a duniyarmu a yau, sannan su kwatanta da yadda suke kallonsu a yanzu. Duk yadda ka ɗora Obasanjo a faifai, babu abin da za ka gani fiye da wata halittar Allah mai ban mamaki. Domin a lokacin da dattawa irinsa ke da fuska ɗaya suke kuma riƙe darajarsu da kimarsu, shi kuwa Obasanjo fuskokinsa sun fi dubu!

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Kuɗaɗen Paris Club: Tsugune Ba Ta Ƙare Ba

Next Post

BABBA DA JAKA

Labarai Masu Nasaba

MUKALAR LITININ: Guguwar ’Yan A Kwafe – A Watsa A Yanar Gizo ‘Copy and Paste’

MUKALAR LITININ: Guguwar ’Yan A Kwafe – A Watsa A Yanar Gizo ‘Copy and Paste’

by
4 years ago
0

...

Tunaninka Kamaninka: Yaushe Za Ka Zama Attajiri?

by
5 years ago
0

...

Badaƙalar Maina: Tsakanin Dambazau Da Oyo-Ita, Wane Ne Mai Gaskiya?

by
5 years ago
0

...

Me Ya Janyo Taɓarɓarewar Harkar Tsaro A Abuja?

by
5 years ago
0

...

Next Post

BABBA DA JAKA

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: