Connect with us

SIYASA

Obasanjo Ba Ya Kishin Arewa, Munafuki Ne Tuburan -Kirfi

Published

on

Wani dattijo a yankin Arewa wato Muhammad Bello Kirfi ya bayyana cewar ko kadan tsohon shugaban kasar Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo bai taba son Arewa da kuma jama’an Arewa ba; yana mai bayanin cewar Obasanjo munafuki ne kawai amma a kowani lokaci babban burinsa ya kashe Arewa da kuma dukkanin ci gaban da Arewa take tunkaho da shi.

Bello Kirfi wanda shine Wazirin Bauchi, ya bayyana hakan ne a lokacin da ke jawabi a wajen bukin taya murna da aka shirya wa mataimakin shugaban jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Babayo Garba Gamawa domin taya sa murnar samun kujerar mataimakin shugaban PDP da ya yi, taron wanda ya gudana a ranar Asabar a Bauchi.

Bello Kiri ya qara da cewa, Cif Obasanjo ya yi aiyukan da suka mamaye zukatan wasu nagartattun mutanen Arewa, amma sai bai kamata jama’an Arewa su yarda da shi kamar yadda suka yarda da shi a baya ba, yana mai cewa ya kamata ‘yan Arewa su yi watsi da dukkanin wani yunkurinsa.

Ta bakin Bello, “Mun samu wahala wanda yake an yi kuskure tun da farko da shuwagabaninmu na Arewa suka kawo mana Obasanjo ya zama mana shugaban kasa; wannan babbar kuskure ne, kuma ana ji ana gani ga irin halayensa, baya sonmu qarya yake yi koda ya ce yana sonmu qarya ya ke yi. Amma yana da mutane wadanda suke na gaban goshinsa,” In ji Muhammad.

Alhaji Bello ya daura da cewa, “Shi Obasanjo yau yana nan gobe yana can, har ya yi abubuwan da suka jawo wa PDP cin mutuncin, ya rage wa PDP kima, yanzu kuma sai ga shi wasu muhimman mutanen Arewa sun dauke shi a matsayin mutum, suna ganin kamar shi ne mai nadin shugaban kasa, ko kuma wani abu na daban,”

Bello Kirfi ya bayyana cewar hatta shugaban kasa mai ci yana biyayya wa Obasanjo “Amma da yake shi Obasanjo ba mutum ne mai kunya ba, ya dauki katin PDP ya yaga wai ya shiga wata jam’iyyar ta daban,”

Kirfi ya bayyana cewar ko kadan Obasanjo bai son ci gaban Arewa da jama’an Arewa, yana mai bayanin cewar “Shine ya kawo mana Jonathan, shi ne kuma ya kawo mana Gwamnan Katsina na da, ‘Yar’Aduwa, ya dauko Jonathan ya hadasu, a tsammaninsa ‘Yar’aduwa ba zai kai wata shida na mulki ba, sai Jonathan ya amshi mulki kasa tun da Jonathan yaro ne sai ya ci gaba da juya sa yadda ya ga dama. Saboda haka sai Allah ya sanya muka karbi ‘Yar’aduwa hanu biyu-biyu, na kuma tabbata da ‘Yar aduwa na raye har yanzu da Nijeriya ta fi haka ci gaba,” In ji Bello Kirfi.

Bello ya gargadi dukkanin ‘yan siyasar Arewa da cewar kada su sake amincewa da kuma yarda da Obasanjo kan kowani abu da ke shirin cewa zai kawo ci gaba wa kasar nan.

Bello Kirfi ya bayyana cewar akwai gayar bukatar a yi zaben cancanta ba wai jam’iyya ba, ya bayyana cewar matukar jama’an qasar nan suka sake yin kuskuren zaben zaben jam’iyya ba dan takara ba, to tabbas akwai matsalolin rashin ci gaba.

Bello ya bayyana cewar shi Uba ne ga kowace jam’iyya a yanzu, amma ya bayyana cewar bai taba yankan Karin wata jam’iyya baya ga PDP ba, sai dai ya bayyana cewar a yanzu haka dai ba zai bayyana cewar kai tsaye shi dan PDP cikakke bane, amma dai ya yi nuni da cewar shi bai da wata kati baya ga na PDP har zuwa ranar da ke Magana a wajen taron.

Tun da fari ma ya bayyana cewar “Ina tabbatar muku maza da mata wadanda suke kishin Arewa mafiya yawansu kuma muhimmai suna cikin jam’iyyar PDP ne, a lokacin da aka samu barna da kuskure na tausaya wa wadanda suke ciki, na yi ta tunanin yadda za a yi a samu jam’iyyar ta ci gaba,” Kamar dai yadda ya shaida.

Haka shi ma wani tsohon Kakakin PDP na jihar Bauchi, Bashir Bukar Rimin Zayam a cikin hirarsa da LEADERSHIP A Yau yake shaida cewar Obasanjo ba mutumin arziki bane, domin mayaudari ne kuma ya yaudari ‘yan qasar nan kawai yake yi.

Ya ce, “Ai Obasanjo mayaudari ne, Obasanjo bai son Arewa, Obasanjo kule a cikinmu.

Don haka ‘yan siyasar yanzu zai yi wuya su gane hakan, mutum ne ya ce bu-yace-me, amma tabbatacce Obasanjo baya son Arewa, amma lokaci zai zo da jama’a za su gane komai, Obasanjo ya yi mana auren dole, ya san ba’a so ya yi mana, ya kuma yi mana abubuwa da yawan gaske. Amma Allah ba zai barshi ba,” In ji Rimin Zayam.

Advertisement

labarai