Connect with us

WASIKU

‘Obasanjo Mai Abin Mamaki’

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A, ina so ku bani dama  na fadi  damuwata a kan tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Ya kamata Obasanjo ka san cewa al’ummar Nijeriya ba su yadda da binciken da hukumar EFCC taima lokacin mulkin Umaru Musa ‘Yar’Aduwa ba. Kaf duniya ta san cewa ka kawo Umaru Musa ‘yar Aduwa ne domin ya rofama asiri saboda barnar da ka aikata.

Yana da kyau ka daina kafa hujja da cewa majalisar dokoki da hukumar EFCC sun wanke ka a kan kudin gyaran wutan lantarkin Nijeriya  a zamanin mulkin Umaru Musa ‘yar Aduwa. Domin babu abin da  ya hada mulkin Baba Buhari da mulkin Umaru musa ‘yar Aduwa.

Kowa ya sani ba talakawa bane suka zabi Umaru Musa ‘yar Aduwa a matsayin Shugaban Nijeriya, kawai ka dora shi domin san zuciya irin na ka.

Ita kuma gwamnatin Baba Buhari jama’ar Nijeriya ne suka hada karfi da karfe suka tabbatar da ita a zaban 2015. Kowa ya san talakawan Nijeriya ne suka fito suka Zabe Baba Buhari a matsayin shugaban kasan Nijeriya.

Ya kama ta Obasanjo ka sani cewa duniya ta san ka ci kudin gyaran wutan lantarkin Nijeriya domin kaima ka tabbatar da  hakan.

Jama’a ku ji irin furicin Obasanjo, daga ranar da shugaban  kasan Nijeriya Muhammadu Buhari ya ta da maganar kudin gyaran wutar lantarkin Nijeriya sai ya ce

“1. Majalisar dokokin Nijeriya sun wanke ni.

  1. Buhari ka je ka duba littafina da na wallafa za ka ga yadda a ka yi da kudin gyaran wutan lantarkin Nijeriya.
  2. Buhari ‘jahili’ ne kai shi ya sa ba za ka fahimci yadda a ka yi da kudin gyaran wutan lantarkin Nijeriya ba.
  3. Hukumar EFCC ta gama bincikana a kan kudin gyaran wutan lantarkin Nijeriya”

Jama’a don Allah mutun mai gaskiya zai dunga tukka da warwara ne?

To maganar gaskiya shi ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ka kama Obasanjo domin ya amayar da dukiyar da ya sata na gyaran wutan lantarki.

Sako daga Usman Hamisu, Kaduna.

08160874213

 

  • Idan Ba Baba Buhari Ba, Wa Za Mu Zaba 2019?

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya.

Duk da cewa yawan kuri’armu ita ce ake la’akari da ita, wannan bai hana a yi tsarin karba-karba ba.

Tsarin karba-karba ba PDP ce ta kawo tsarin nan ba, wani bangare ne na kasar nan ne cewa hakan ba dai- dai bane. La’akari da wannan ne nake cewa in ba Buhari ba to waye zabin mu?

Idan Buhari yayi shekaru hudu, to abin tanbayar a nan Shi ne sauran shekaru  hudun na waye?

Amsar tambayar dai ita ce har yanzu sauran shekarun hudu na bangaren Arewa ne. To a duk Arewa waye ya kai Buhari nagarta da zamu ba shi sauran shekarun Hudu?

Idan muka ce zamu dauko wani daga Arewa shin kuna ganin akwai wanda zamu zaba da zai iya alkawarin cewa shekara hudu kacal zai yi kuma ya cika alkawarin ya sauka a duk Arewa?

Amsa ita ce babu kawai, don haka Buhari dai Shi ne mafita ga al’ummar Nijeriya ko ka so ko ka ki shi ne mai iya cika alkawari.

Sako daga Muhammad Idris (Babanne), Abuja.

07065279510 

 

  • Matsalar Gwamnati Ne Da Al’ummar Yankin Jihar Kaduna

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jinni baki daya.

Ni fa har yanzu a Nijeriya ba abun da yake kulle mun kai, ya hanani fashin baki kamar lamarin ta’addanci a yankin Binnin Gwari.

Duk wanda ya saurari shirin bbc na ra’ayi riga na wannan makon wanda BBC din ta gabatar a jihar kaduna wato a Sardauna House (gidan arewa). Zai ji yadda al’umma a ciki da wajen jihar kaduna tare da masu fashin baki da kuma wakilan gwamnati a cikin hirar inda aka tauttauna a kan batun. Abun da ya fi jan hankali a cikin hirar, shi ne irin yadda gwamnati ta yi sakaci da yankin ta hanyar wofantar da jami’an ‘yan sanda dana soji zuwa cikin birane ta hanyar da daya daga cikin mazauna yanki ke bayyana rashin koda irin ‘yan sandan nan na waje (out post) da ake sawa a kauyukan.

Baya ga haka daya daga cikin masu magana a shirin mai suna Sunusi ya ce lokacin da aka yi jami’an soji dana ‘yan sintiri magana ya ce gaba ki dayan su ba su fi su 50 ba amma kuma wadan can yan bindigar ya kai kimanin dari uku. Baya ga rashin wadatattun jami’an tsaron ga kuma rashin kayan aikin da jami’an za su fuskance su. (Kamar yadda shugaban nin tsaron suka bayyana a wata ganawar kwannan da kusoshin majalisa).

Gwamnati a yunkurinta na dakatar da rasa rayuka ya sake rusa wani aikin ta hanyar rufe hanya da ga Garin Gwaska Zuwa Birnin Gwari domin Kiyaye war yan bindigar, amma yunkurin gwamnatin ya ci tura ta hanyar da hanyar ta zama kamar wani wajen cin karen su babu bababaka.

Al’umma na gani mutane da ke da hannun a kan su ta hanyar kai musu kayan yau da kullum kamar abincin su da kuma wani abun bukata. Alhalin mutane suna sane da irin illar ga al’umma.

Dole ne mu tashe tsaye mu tsaya tsayin daka wajen ganin an kawo karshen Kashe-Kashen Al’umma da kuma dukiyoyin al’umma ta hanyar Addu’o’i  da kuma daukan matakan da suka dace.

Sako daga Falalu Abdullahi, Zariya.

07032933355

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: