Sabo Ahmad" />

Obasanjo Ya Fara Koyarwa A Jami’ar NOUN

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya samu damar koyarwa a jami’ar NOUN, yayin da aka ba shi lura da ofishi da zai gudanar da aikinsa a Cibiyar  jami’ar da ke garin Abeokuta ta jihar Ogun ranar Talatar da ta gabata.

Shugaban jami’ar Farfesa, Abdalla Adamu,ya ba tsohon shugaban kasar wannan aikin ne bayan kammala digirinsa na uku da ya yi a jami’ar.

Obasanjon zai ci gaba  duba dalinan wannan jami’a daga lokaci zuwa lokaci.

Mista  Obasanjo, shi ne dalibin jami’ar na farko da ya samu digiri na uku fannin nazarin tauhidi a addinin Kiristanci wanda kuma aka ba shi shaidar kammala karantun nasa a wajen bikin yaye daliban jami’ar karo na bakwai, wanda aka yi a abuja.

Shugaban Cibiyar jami’ar ta Abeokutan, Ibrahim Salawu, ne ya nuna wa Obasanjo ofishin da zai ci gaba da gudanar da aikinsa.

Haka kuma Mirta Salawu,ya zaga da tsohon shugaban kasar tare da ‘yan tawagarsa domin nuna masa harabar cibiyar, wanda kuma ya nuna jin dadinsa da kasancewar samun tsohon shugaban kasar a mtsayin abokin aiki wanda zai taimakawa cibiyar jami’ar wajen samun ci gabanta. Saboda shi ma tsohon shugaban kasar ya nuna jin dadinsa da wannan dama da aka ba shi. Sann da cikkakiyar gudummawarsa wajen samar da ci gaban wannan cibiya.

 

Exit mobile version