Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, na shirin zuba jarin dala miliyan 700 a Kamaru domin bunƙasa kasuwanci tsakanin Nijeriya da Kamaru.
Ana sa ran Obasanjo zai kai ziyara tashar ruwan Kribi a watan Afrilu domin ƙaddamar da kamfaninsa, Obasanjo Agro-Allied Business Ltd (OABL).
- Allah Ya Yi Wa Galadiman Kano, Abbas Sanusi, Rasuwa
- Duk Da Hanin Gwamna Da ‘Yansanda, Natasha Ta Isa Gida Kuma Ta Yi Taro
Wannan shiri zai taimaka wajen inganta harkokin noma, sufurin ruwa, da masana’antu a yankin.
Shugaban kamfanin Aftel Cameroon Limited, Agha Albert Ngwana, ya bayyana cewa jarin da Obasanjo zai zuba zai ƙunshi noma, sufurin ruwa, da samar da kayayyaki kamar taki da itace.
Obasanjo zai yi noma a fili mai faɗin hekta 610, inda zai dasa masara da waken soya domin tallafa wa kasuwancin kiwon dabbobinsa.
Haka kuma, yana shirin gina masana’antar sarrafa itace da samar da sabbin hanyoyin ruwa domin rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Lekki.
Wannan jari ya zo ne a daidai lokacin da Kamaru ke faɗaɗa tashar jiragen ruwa na Kribi domin ƙara inganta kasuwanci a yankin.