Ohanaeze Ta Jinjina Wa  Obiano  Kan Jirgin Saman Da Ya Fara Sauka A Anambra

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta duniya baki daya ta taya murna tare da jinjinawa gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano da daukacin mutanen Jihar kan jirgin sama na farko wanda ya fara sauka a filin jirgin sama na Umueri Anambra, a ranar Juma’a, 30 ga Afrilu, 2021.

kungiyar ‘yan-kabilar Igbo, a cikin wata sanarwa da Sakataren ta ma yada labarai na kasa, Cif Chiedozie Aled Ogbonnia,  kungiyar ta bayyana  jin dadin ta game da hangen nesa, jajircewa, karfin gwiwa, himma, da kuma kwazo wanda Obiano ya yi aikin filin jirgin saman har zuwa lokacin daya fara aiki.

“A lokacin da Kungiyar Ohanaeze Ndigbo, a karkashin jagorancin Farfesa George Obiozor, ta ziyarci wurin a ranar 18 ga Maris, 2021, Obiozor ya bayyana filin jirgin saman kasa da kasa wanda ya fara aiki na Anambra da ke gudana a matsayin wani  matsayin wani babban aiki ne, wanda  ba zai tsaya a bunkasa tattalin arzikin tattalin jihar Anambra ba kadai, har ma daukaci shi sashen na  Kudu maso Gabas.

Ya kara da cewa  a lokacin daya samu kammala babbar kasuwar Onitsha wadda zata kasance  babbar kasuwa a sashen  Afirka ta yamma, wannan wani matakine wanda zai dade a zuciyar kabilar Ibo, har ma ga wadanda ba a kai ga haihuwarsu  yu ba.

Obiozor ya bayyana cewar cike yake da farinciki a matsayin na wanda bai  taba ganin irin wannan ci gaban ba ba,  sai a kakashin mulkin gwamnatin Obiano, kamar yadda ya bayyana.

Ogbonnia ya  kara da cewa abubuwan da suka kasance a filin jirgin ya nuna jajircewar gwamnan wajen cika ka’idojin kasa da kasa kamar yadda yake a sauaran wurare.

“Gwamna Obiano ya bayyana cewa ya yanke shawarar fara aikin filin jirgin saman ne, saboda la’akarin da ya yi na cika burin wadanda suke da shi al’amarin bunkasa tattalin arziki a zuciyar su.

“Ya bayyana cewa filin jirgin saman yana da titin da jirgin zai yi tafiya kafin ya kai ga tashi  mafi tsayi, kuma na biyu a Nijeriya bayan Filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas. Obiano  shi ma da kan shi ya nuna jin dadinsa ganin cewa filin jirgin ya fara aiki ne a watan Afrilu na shekarar 2021. ”

Exit mobile version