kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta Inyamurai zalla ta nuna jin dadinta akan nada sababbin shugabannin rundunonin tsaro na soja wanda ya yi a wannan makon da muke ciki.
Shugaban kungiyar Farfesa George Obiozor shi ne ya bayyana jin dadin ‘yan kungiyar, a wata sanarwar da yaba manema labarai a Enugu ranar Alhamis.
Maneama labarai sun bayyana cewar nada su sababbin shugabannin rundunonin da Buhari ya yi ranar Talata akan Manjo janar Lucky Irabor, shugaban rundunar tsaro, Manjo janar Ibrahim Attahiru, shugaban rundunar sojoji, Rear Admiral Awwal Gambo shugaban rundunar sojojin ruwa, ya yin da kuma AbM Isiaka Amao shi ne shugaban sojojin sama.
Obiozor ya bayyana cewar shi wannan nadin za a dade ana tunawa da amfanin shi, wanda kuma hakan ne zai ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewar, shugaban bada wasa yake ba, kuma shirye yake ya yi maganin matsalolin tsaro, wajen bullo da wasu tsare- tsare.
Muna matukar farin ciki mun gode ma shi musamman ma “Nada Manjo janar Lucky Irabor shi janar ne da kowa ya yi na’am da harkokin shi.
Dan Majalisar Tarayya Ya Sabunta Katin Jam’iyyar APC A Funtuwa
Daga Hussaini Yero, Funtua Dan majalisar Tarayya me wakiltar mazabar...