‘Okay’ Din Ciyaman, Sam Nda-Isaiah (2)

Sulaiman Bala Idris

Ci gaba daga makon da ya gabata…

…Har Malam Musa ya tafi hutun karshen mako Kaduna, muka yi waya, ya ce na shirya gobe Juma’a na tafi Abuja. Na shirya na tafi. Na je gidan Ciyaman, zuwan farko. Ina shiga ya fara fara’a, ya ce, ‘So, kai ne ka yi LEAD story din nan? Kana da future, ka ci gaba da kokari’. Ni dai shiru kawai na yi. Sai ga Dabid Chinda (mutumin kirki) ya shigo falon. Chinda shi ne Babban Manajin Darakta na Kamfanin Kadarorin LEADERSHIP.

Tun kafin Chinda ya zauna, sai Ciyaman ya tari numfashinsa, ya ce, “Na kira Minista kan ‘relocation’ din Sulaiman, ka bi sahun maganar.” Ni dai ina zaune wuri guda. Nan da nan Chinda ya karbi lambar wayata, ya kuma ce na adana tasa. Na bar gidan Ciyaman gab da la’asar, na shiga cikin gari na yi wasu hidindimu sannan na koma Kaduna cikin dare. Lokacin ba a fara fargabar bin hanya ba kamar yanzu.

Ranar Litinin na shirya muka koma Abuja don fuskantar wannan babban aiki. Ni dai ban ji labarin an sauya min wurin yi wa kasa hidima ba. Sai da muka je Abuja, muka yi haduwar farko da Manajin Darakta dinmu ta farko, wata baiwar Allah mai taka-tsantsan da sanin ya-kamata, Madam Tina. Tana son aiki cikin tsari, tana son tsafta, tana kuma son jajircewa. Dukkaninmu a lokacin, Malam Musa Muhammad, Ni, Abdulrazak Yahuza Jere, Mubarak Umar, Nasir Gwangwazo mun fahimci cewa, dole sai mun dage kafin mu iya yin aiki da Madam Tina.

Da Madam Tina muka yi ta shirya yadda LEADERSHIP A Yau za ta kasance. Burinta shi ne ta yi wani abu na musamman kamar yadda Ciyaman ya bukata. A gabadaya LEADERSHIP babu wanda ke iya yin musu ko gardama da Ciyaman, amma Madam Tina tana iyawa. Idan ta ga an yi abin da bai dace ba, nan take ta ke yin gardama, ta kuma cewa Ciyaman ba zai yiwu ba.

Bayan kamar wata guda da fara wannan shiri, sai na tada kayar baya akan lallai fa a yi wani abu a kan batun ‘relocation’ dina na NYSC. Saboda zan iya samun matsala. Madam Tina ce ta kira Ciyaman kaitsaye. Nan fa ya hau fada akan me ya sa tuntuni ba a yi wannan abin ba. Gari na wayewa sai Babban Manajin Daraktan Kamfanin LEADERSHIP na lokacin, Abdul Gombe ya kira ni a waya. Ya ce, an ce na duba shafina na NYSC. Ina dubawa na ga har an cika aiki, an dawo da ni Abuja. Kwanciyar hankalin da na fara samu kenan na farko.

Hankalina ya tashi lokacin da Madam Tina ta ajiye aiki. Gabadayanmu mu biyar Malam Musa, da sauran Editoci hudu sai da gwiwarmu ta yi sanyi. Saboda mun so yin aiki tare da ita, musamman bisa la’akari da yadda ta ke kishinmu, ta ke kuma tsaya mana kan komi. Wannan bai sa mun daina shiri ba, a haka aka ci gaba.

Kwatsam! Watarana sai muka wayi gari da sanarwa daga Ciyaman, wacce ke cewa Stanley Kingsley ya maye gurbin Madam Tina a matsayin Manajin Daraktan LEADERSHIP A Yau (Jaridar hausa ta farko da za ta rika fitowa kullum).

Stanley Inyamuri ne mai hazaka, kuma wanda ke jin hausa. Stanley ba ya manta halasci, watarana ya taba fada mana cewa, ko da Ciyaman zai yi mishi korar Kare a LEADERSHIP, ba zai taba iya bude baki ya zage shi, ko ya aibata shi ba. Domin kuwa Ciyaman ya yi mishi abin da bai taba tsammanin wani zai iya yi masa a duniya ba.

A ranar da muka fara aiki, 11 ga watan Satumbar 2017, Ciyaman yana Kasar Chana. Ga shi kuma ni ne Editan da ya fara aiki ranar wannan Lahadin kan jaridar da za ta fito Litinin. Stanley na tare da mu har dare. Da na kammala aiki sai aka ce ai Ciyaman ya bayar da umurni, kullum a tura mishi da PDF na shafukan jaridar kafin a tura ga dab’i. Ni kuma bani da lambar Ciyaman, ba ni da I-mel dinsa.

Nan take Stanley ya bani I-mel din Ciyaman, na tattara gabadaya PDF din jaridar, na tura. Ina zaune, sai ga Stanley ya sake shigowa, ya tambaye ni ko na yi magana da Ciyaman. Sai na ce mishi ai ba ni da lambarshi, shi ya kira shi. Sai ya ce, min ai ni ne ya fi dacewa da na kira shi.

Stanley ya bani lambar Ciyaman. Kafin na kira sai na tura da sakon tes na gabatar da kaina. Sannan na kira. Yana dauka, ya dan yi kinkinar nan (dama Ciyaman yana kinkina), ya ce, ‘Ya dai?’ na ce, lafiya lau, ‘na tura ma I-mel na jaridar gobe’.

Bayan kamar minti 30 sai ga Stanley ya sake dawowa, ya tambaye ni ya ake ciki. Na fada mishi na yi magana da Ciyaman, amma har yanzu dai babu wani sabon umurni daga gare shi. Sai Stanley ya kira Ciyaman a waya, yana dauka kuwa ya ce mishi ai ya bada umurnin a ci gaba da aiki. Ko da Stanley ya katse wayar, sai ya ce min, ban ga sakon tes daga Ciyaman ba ne, sai na ce mishi na ga ya turo min da ‘OKAY’. Ai kuwa, sai Stanley ya fashe da dariya!

Zan ci gaba mako mai zuwa

 

Exit mobile version