Ci gaba daga makon da ya gabata.
Stanley ne ya fada min cewa ai idan ka tura wa Ciyaman aiki ya turo maka da sakon ‘Okay’ yana nufin an baka izinin ka ci gaba kenan. Ya dan qara min da wasu shawarwari game da wanne irin mutum ne Ciyaman, kuma ya ake zama da shi. Daga cikin abin da na riqe sosai akwai batun cewa, Ciyaman na so ka riqa takura mishi idan ya sa ka aiki; wanda a hankali na fahimci wannan.
Gabadaya labarin fushi da hayaniyar Ciyaman na ke ji a wurin wasu kafin wata ranar Talata, bayan mun yi kamar watanni hudu da fara aiki. Sai masu aikin kwamfuta suka hade kai suka ce ba za su yi aikin Jaridar Laraba ba, har sai an biya su albashinsu na wata biyu. Duk da na san da shirinsu, ni dai ban yi qasa a gwiwa wurin ci gaba da hada aiki ba, har zuwa yamma. Sannan ne na sanar da Stanley cewa, zan kira Ciyaman na sanar da shi halin da a ke ciki, domin kuwa idan har na yi shiru jaridar washegari ba ta fito ba, zan kasance cikin manyan masu laifi.
Hankalina a tashe na sake kiran Stanley, na sanar da shi yadda muka yi da Ciyaman. Nan da nan ya garzayo ofis. A haka aka yi ta maida magana tsakanin manyan ma’aikatan kamfanin. Wasu daga cikinsu sun yi ta ganin laifina akan bai kamata na sanar da Ciyaman halin da a ke ciki ba, domin su ya yi wa dirar mikiya. Amsa daya na yi ta ba su, “Idan jarida ba ta fito ba, ni ne Edita, kaina za ta qare.”
Tun farkon fara aikin, a duk lokacin da muka hadu da Ciyaman yabonmu ya ke yi. Wasu lokutan ma sai na dan ji kunya, yadda ya ke caccakar sauran ma’aikatan sashen turanci. Ya riqa cewa, Yara sun zo sun fi ku sanin kan aiki. Wannan yabo da jinjinawa ta Ciyaman ta ja mana tsangwamar da ba iya bayyanata a fili, sai dai a bizne ta a zuciya.
Lokacin da aka zo maganar tafiya aikin Hajji na shekarar 2018 aka sanar da ni cewa ni ne zan tafi. Tabbas na ji dadin shaida biyu da aka bayar. Ta farko, Babban Manajin Daraktan LEADERSHIP, Abdul Gombe ya tambayi Shugabar sashen kudi shin idan ana so a karrama wani a sashen Hausa, wa ta ke ganin ya kamata. Sai ta kira sunana. G.M.D ya tambayeta ko mene ne dalili. Sai ta ce: “Bai taba cewa BA ZAI YIWU BA. Idan ka tambaye shi yaushe za a kawo aikin kudi, zai ce kudi sun kusa zuwa. Kuma yana kawowa din.”
Shaida ta biyu ita ce ta Ciyaman. Ko da na kira don sanar da shi cewa zan tafi Hajji. Idan kuma bana nan, Mataimakina na lokacin (Editan Jaridar LAHADI a yanzu), Malam Bello Hamza zai riqe aikin har na dawo. Cikin harshen Ingilishi Ciyaman ya ce, “Ai na fada maka, gobenka tana da haske. Kuma za ka yi nisa a wannan harkar. Ka ci gaba da dagewa.”
Allah Sarki! Akwai watarana da na tafi Kano zance, lokacin ban yi aure ba. Na isa Kano ranar Juma’a, ina gidan su Matata da yamma sai ga kira daga Ciyaman yana tambayata ko ina gari. Na ce, mishi a’a, har da ‘yar guntuwar qarya, na ce ina Kaduna alhali ina Kano. Sai kuwa ya ce, na zo yana nema na. Na ce, toh. Har ga Allah na yi niyyar na bari sai Lahadi sannan zan je na same shi. Ranar Asabar da safe sai ga kira daga Geoffrey (mutumin da ban taba ganin mai ji-ji da kai irinsa a LEADERSHIP ba), ya buqaci na tura masa adireshin I-mel dina. Ban ma tsaya tambayarsa dalili ba, na tura.
Bayan La’asar sai ga saqon I-mel daga Geoffrey, wai umurni daga Ciyaman, na zama Editan Jaridar LEADERSHIP ta turanci. Ina gani na kira Geoffrey a waya, na ce mishi ba zan yi ba. Nan fa ya harzuqa, ya fara fada, yana cewa ai sai na kira Ciyaman na sanar da shi, “Kuma ka kwana da sanin babu wanda ya isa ya qi amsar umurnin Ciyaman.” Na katse shi mishi hanzari, na sake cewa, ba zan yi ba, zan kira Ciyaman din.
Na kira Ciyaman, yana dauka ya ce, me ya sa har yanzu ban zo ba. Na ce, zan zo, amma wannan takardar muqamin da aka buga bana jin zan yi. Sai ya ce, “don me? Ka zo ina jiranka. Qarfe hudu na yamma na dauki Rabi’u Ali Indabawa muka bar Kano zuwa Abuja. Sai bayan Magriba muka bar Kaduna, ga shi ana ruwan sama, cikin zulumi haka muka yi ta nausawa a hankali. Ba mu shiga gidan Ciyaman ba sai qarfe 11:30 na dare. A nan na kwakkwafe Ciyaman, har ya gamsu. Washegari sai ga sabuwar takarda, an fasa sabon muqamin da aka yi min. Wannan lamarin ya ba manyan ma’aikatan LEADERSHIP mamaki, tun lokacin suke kirana da ‘Mutumin Ciyaman’.
Tabbas! Mun yi zaman arziki da rabuwar arziki da Ciyaman. Duk zafin ransa da saurin fushi, bai taba zagina ba kamar yadda ya ke zazzage ma’aikatansa. Idan na ce ina son yin magana da wani Gwamna, Minista ko babban mutum, lamba yake aiko min. Sannan ya ce, idan na kira ba a dauka ba, na sanar da shi, zai yi min iso. Mako biyu kafin ya rasu ya bani wani aiki da nake ba shi rahoto kullum ta ‘Whatsapp’, hatta ranar Juma’ar da ya rasu sai da na tura. Saqon da bai bude ba kenan, ballantana mu tattauna.