Okonjo-Iweala Ce ‘Yar Afirka Ta Farko Da Za Ta Jagoranci Hukumar Cinikayya Ta Duniya

Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO) ta shirya wani taro na musamman a yau Litinin, inda ake sa ran za a bayyana tsohuwar Ministar Kudi ta Nijeriya, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a hukumance a matsayin babbar Darakta ta hukumar. 

Rahotanni sun bayyana a makon da ya gabata, ajandar taron na yau ita ce, “yin la’akari da nadin sabon Darakta-Janar na WTO.”  Makon da ya gabata ne gwamnatin Amurka ta nuna goyon bayanta ga fitowar Okonjo-Iweala a matsayin Darakta Janar.

Ta kuma yadda ta cire cikas na karshe ga yunkurin ta na zama mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko da za ta gudanar da kungiyar kasuwanci ta duniya a ofishinta dake Geneva.

Okonjo-Iweala a watan Oktoban da ya gabata ta samu nasarar kuri’a na mambobi 163 daga cikin 164 na kungiyar cinikayyar, amma ba a iya ayyana ta a matsayin shugabar WTO ba saboda dokokin zaben kungiyar sun nuna cewa dole ne nasarar tata ta fito ta hanyar yarjejeniya.  Yoo Myung-hee na Koriya ta Kudu, wanda Amurka ke marawa baya, ya kasance abokin hamayyar Okonjo-Iweala bayan wasu ‘yan takarar sun janye daga takarar a bara.

Exit mobile version