OLYMPICS: Brazil Ba Ta Gayyaci Neymar Ba

Neymar

Tawagar kwallon kafa ta Brazil ta bayyana ‘yan wasanni 23 da za su buga mata kwallon kafa a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympic da birnin Tokyo zai karbi bakunci a bana, amma ba Neymar a ciki.

Neymar dan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain, mai shekara 29 a duniya, baya cikin ‘yan wasa uku da aka amincewa tawaga ta dauka wadanda shekarunsu suka haura 23.

Cikin ukun da Brazil za ta je da su birnin na Tokyo dake Japan domin buga mata wasan a Olympic sun hada da tsohon dan wasan Barcelona da Juventus, Dani Albes da Diego Carlos da kuma Santos.

Brazil wadda ke fatan kare zinaren da ta lashe a shekarar 2016, bayan doke ‘yan wasan kasar Jamus, ta zabi Albes ganin cewar yana daga cikin masu sa’a a wasannin kwallon kafa da kan lashewa kungiya ko tawaga kyautuka

Cikin watan Mayu Albes ya cika shekara 38, shi ma yana fatan kara lashe kyautar lambar yabo a Tokyo domin karawa daga wadanda yake da su tun a baya, sannan sauran ‘yan wasa 20 da aka gayyata sun kasance ‘yan kasa da shekara 23, kamar yadda doka ta tanada a gasar kwallon kafa ta Olympic.

Za’a fara gasar wasannin Olympic da birnin Tokyo zai karbi bakunci daga ranar Juma’a 23 ga watan Yuli zuwa Lahadi 8 ga watan Agustan wannan shekarar ta 2021 kamar yadda aka tsara za’ayi.

Tun a bara ya kamata a gudanar da wasannin Olympic, amma tsoron yada cutar korona ya sa aka dage fafatawar zuwa shekarar 2021 kuma har yanzu ana cece-kuce a kasar Japan akan karbar bakuncin gasar tsakanin gwamnati da jami’an lafiyar kasar.

Sunayen ‘yan wasan tawagar Brazil da za ta buga Olympic a Tokyo

Masu tsaron raga: Santos da kuma Brenno.

Masu tsaron baya: Dani Albes da Gabriel Menino da Guilherme Arana da Gabriel Guimaraes da Nino da kuma Diego Carlos.

Masu buga tsakiya: Douglas Luiz da Bruno Guimaraes da Gerson da Claudinho da Matheus Henrikue.

Masu wasan gaba: Matheus Cunha da Malcolm da Antony da Paulinho da kuma Pedro.

Exit mobile version