Abba Ibrahim Wada" />

Omeruo Da Colins Ba Su Cancanci Baga Wa Nigeriya Wasa Ba – Babangida

Omeruo

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Najeriya, Tijani Babangida ya ce bai kamata ‘yan wasan da ke wasa a rukuni na biyu a Turai su samu gayyata zuwa babbar tawagar kwallon kafa ta kasa ba.

Babangida, wanda shine shugaban kungiyar kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya, ya bayyana hakane a wata ganawa da manema labarai ta kafar intanet inda yace idan dan wasa baya buga babbar gasa a kowacce kasa bai cancanta a gayyace shi wakiltar Super Eagles ba.
‘Yan wasa  Kenneth Omeruo da William Troost-Ekong da Jamilu Colins na cikin ‘yan wasan da ke wasa a rukuni na biyu a Turai, kuma har yanzu ke yi wa tawagar Super Eagles ta Najeriya wasa.
“Bai kamata dan wasan da baya buga babbar gasar nahiyar turai ya dinga bugawa kasar nan wasa ba saboda akwai bukatar kwarewa sannan kuma abin kunya ne ace muna da manyan ‘yan wasa amma ace sai muje mu gayyaci wadanda basa buga wasa da manyan ‘yan kwallon duniya” in ji Babangida
Ya kara da cewa “Ita tawagar kwallon kafa manyan ‘yan wasa take bukata wadanda suke buga wasa a babban matsayi a duniya kuma wadanda duniya take kallonsu a matsayin wasu gwaraza wadanda babu kamarsu a wannan kasa”
Sai dai daman tun kafin Tijjani Babangida yayi wannan korafi wasu daga cikin tsofaffin ‘yan wasan kasar nan sunyi korafin cewa bai kamata a dinga gayyatar ‘yan wasan da basa buga manyan gasanni ba  zuwa Super Eagles.

Exit mobile version