Orabe Philips: Matashin Da Ya Rafke Ba’amurke Da Tabarya

Rundunar ‘yansandan jihar Legas ta samu nasarar kama Orabe Philips Leo, da ke zaune a Adeniyi street, Ikorodu, Jihar Lagos, bisa yunkurin kashe wani Ba’amurke,  Mista Robert Rob Wheelers, wanda suka yi aiki tare a Tony Elumelu Foundation a shekara ta 2015.

Ba’amurken ya zo Nijeriya ranar 25 ga Agusta, 2017, wanda tun daga saukarsa a filin jirgin saman Leo ya dauke shi, bai ajiye shi a ko’ina ba, sai a gidansa da ke Ikorodu, in da zai zauna kafin ya koma. A nan ne mai masaukin bakon Leo, ya yi yunkurin kashe Wheelers, wanda hakan ta sa ya bar shi kwance cikin jini, shi kuma zakara ya ba shi sa’a.

Ganin halin da Wheelers ya tsinci kansa a ciki, sai aka sanar da ‘yan sanda, wadanda kuma nan da nan suka zo, suka dauki Wheelers zuwa asibiti don ceton ransa. Sannan suka dawo suka baza ashiftar neman Leo ruwa a jallo, wanda kuma suka samu nasarar cafke shi ranar 8 ga Satumban 2017 a wata maboyarsa da ke Ikorodu.

Binciken da ‘yan sanda suka yi, Leo ya amsa laifinsa, domin kuwa ya tabbatar musu da cewa, ya buga wa Wheelers tabarya akansa har sau uku, saboda ya ki cika masa alkawarin da ya yi na ba shi wadansu kudi wanda kuma shi ya sa rai da su sosai, a kan biyan wadansu bukatunsa.

A karshe, Leo ya cigaba da shaida wa ‘yan sanda cewa, kafin ya afka wa Wheelers, sai da ya samu asiri a wata coci, wanda idan ya tambaye shi zai ba shi kudin, amma da ya tambaye shi sai ya ki ba shi, wannan na daga cikin abin da ya kara fusata shi har ya kai ga yunkurin kashe shi.

Exit mobile version