Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Napoli, Gannaro Gattuso, ya tabbatar da cewa likitocin kungiyar sun gaya masa cewa dan wasan gaban kungiyar, dan Nigeriya, Bictor Osimhen yana ci gaba da murmurewa daga ciwon da yaji a kafadarsa.
Osimhen dai ya dade yana jinya sakamakon ciwon da yake fama dashi a kafada wanda ya hanashi bugawa kungiyar wasa na watanni kuma a cikin tawagar Nigeriya ya samu raunin a lokacin da yake atisaye da ragowar ‘yan wasan Super Eagles.
Bugu da kari dan wasan ya kamu da cutar Korona a lokacin da yazo gida bikin Kirsimeti da kuma bikin murnar zagayowar haihuwarsa sai Napoli ta tabbatar da cewa za a sake yi wa dan wasan gwajin cutar Korona saboda har yanzu cutar ba ta rabu da shi ba.
Gwaji ya tabbatar dan wasan mai shekarau 22 ya harbu da cutar cobid 19 ne jim kadan bayan dawowarsa daga Najeriya, inda ya je hutun Kiristimeti kuma tuni aka killace shi kamar yadda dokar hukumar lafiyar kasar ta tanada.
Osimhen ya kebe kansa na tsawon kwanaki 14, amma bayan an sake gwada shi sai aka ga burbushin cutar a tattare da shi wanda yake nuna cewa cutar tana tare dashi har yanzu bugu da kari kuma yana fama da ciwo a kafadarsa.
Tun bayan komawarsa kungiyar ta Napoli daga Lille, Osimhen ya zura kwallaye biyu a raga sannan kuma ya taimaka an zura kwallaye hudu cikin wasanni tara daya bugawa kungiyar a kakar wasa ta bana.