Connect with us

RAHOTANNI

Osinbajo Ya Bukaci Masu Zuba Jari Su Kara Neman Ilimi

Published

on

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya shawarci masu zuba jari su kara neman ilimi a kan fannin kasuanci yadda zasu nuna cewar a shirye suke wajen son cin nasarar tatalin arezikin kasar nan. Yemi da Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN, Godwin Emefiele, Shugaban Bankin  Zenith Bank Plc, Jim Obia da sauran kararru a fanin hada-hadar kudi ne suka bayar da shwarar a ranar Litinin data gabata a jihar Legas a lokacin kaddamar da littafi da Obia ya wallafa mai taken: Afirka ta farfado tana haskawa. Mataimakin Shugabar kasar ya kuma jinjinawa Obia akan wallafa littafin don wayarwa da sauran kai akan yadda zasu inganta kasuwancinsu. Ya yi kira akan kada a mayar da hankali akan adadin kadai, amma su mayar da hankali akan abinda littafin ya kunsa. Ya kara da cewar, labarin Bankin na Zenith labara ne na sanya kula da mayar da himma. Shi kuwa Gwamnan Babban Banki Emefiele, ya bayyana cewar, dole ne a sanya masu zuba jarin akan ka’idoji yadda zasu kasanace na da ban kuma wadannan ka’idojin sun hadada, ilimi, dagewa yadda zasu kaucewa yadda wasu suka gaza. Yaci gaba da cewar, kamar yadda kuka gani a cikin littafi, wadannan ababen zasu taimaka wajen mini wajen yin hadaka na dala biliyan sha shida daga kimanin naira miliyan biyu don fara kasuwancin. Acewarsa, ga wasun mu da suka yi akiki a karkashin Mista Jim Obia, shi Rumbu ne na ilimi wanda kuma yi yi zurfi wajen mayar da hankali akan abinda ya sanya a gaba. Ya kara da cewar, wadannan ababen sunada mahimmanci yadda zasu bawa masu zuba jari na kasar waje tunkarar kasuwar nahiyar Afirka domin abinda yafi dacewa shine masu zauba jarin su fahimci alfanun dake a cikin kasuwar yadda zasu amfana da fannin fasaha da kuma kirkire-kirkire don samar da manyan kaya da aiwatar da ayyuka ga kasuwa ga kimanin mutane miliyan 200 kamar a Nijeriya.  Ya bayyana cewar, idan akabi wadannan ka’idojin na Mista Jim Obia ya yi a Nijeriya da suran sassan duniya za’a samu dimbin sakamako akan kokarin nasa. Shi kuwa Obia yace, ya rwallafa littafin ne don yadda yanayin Afirka yake ganin cewar Nahiyar cike take da yawan yin juyin mulki, cin hanci da rashawa gabnin cewar kuma za’a iya zuba dimbin jari a nahiyar. Yace, ya mayar da hankali ne ga Najiriya akan yadda za’a bayar da dama wajen yin kasuwanci. Yace, idan muka dora dora tattalin arzikin kasa akan fannin fasaha, za’a samu ci gaba, musamman a fannin aikin noma, kiwon lafiya zamu san irin alfanun da hakan zai kawo. Obia ya yi nuni da cewar, Afika tanada kwarewa a cikin shekarun da suka wuce. Acewasa, “ gare ni Afirka tana tasowa domin a cikin shekaru ashirin dasuka wuce, kasashen Afirka sun mallaki wayar tafi da gidanka, fannin kimiyya da kafar sadarwa ta internet. Manyan fannonin da suka fito daga fannonin tattalin arzikin kasa da kuma sarakunan gargajiya sun halarci taron na kaddamar da littafin

Advertisement

labarai