Connect with us

LABARAI

Osinbajo Ya Rubuta Wa Babban Sufeto Korafi Kan Karyar Da Aka Yi Masa

Published

on

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya rubuta takardar korafi zuwa ofishin babban sufeton jami’an ‘yan sanda (IGP), Muhammad Adamu, domin neman a binciki ma su alakanta shi da karbar kudi daga hannun Ibrahim Magu.
Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dakatar, ya na fuskantar tuhuma ne akan almundahana da barnatar da kudade da kadarorin da hukumar ta kwace.

kafar yada labarai ta yanar gizo, PointBlank, mallakar Jackson Ude, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ta wallafa rahoton cewa Magu ya barnatar da naira biliyan N39 tare da bawa mataimakin shugaban kasa naira bliyan N4 daga cikin kudin a matsayin toshiyar baki.
Rahoton ya yi ikirarin cewa wata majiya ce daga cikin kwamitin binciken Magu ta sanar da jaridar labarin bawa Osinbajo kudin.

“Magu ya sanar da kwamitin bincike cewa ya bawa mataimakin shugaban kasa naira biliyan N4 bisa umarnin shugaban kasa a ranar da zai bar Najeriya zuwa kasar Ingila domin zaman jinya,” a cewar wani bangare na rahoton jaridar Pointblank.

Sai dai, rahoton jaridar bai bayar da cikakken bayani a kan wacce tafiya ne shugaba Buhari ya bayar da umarnin ba, saboda shugaba Buhari ya ziyarci kasar Ingila domin a duba lafiyarsa fiye da sau daya.

A cikin wasikar da Osinbajo ya rubutawa IGP ranar Laraba ta hannun lauyansa, Taiwo Osipitan, ya bayyana rahoton a matsayin kage da sharri domin bata ma sa suna, a saboda haka ya bukaci a bi ma sa hakkinsa.

Haka Kuma, Yemi Osinbajo ya aika kwafin wasikar zuwa ofishin ministan shari’a, Abubakar Malami.

Mai Magana da yawun mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, Laolu Akande yace babu alamar gaskiya acikin ikirarin jaridar.
Advertisement

labarai