Mukaddashin shugaban Nijeriya Yemi Osinbajo ya umarci manyan Hafsoshin sojojin kasar da su gaggauta komawa birnin Maiduguri, don cigaba da fafatawa da ‘yan Boko Haram.
Osinbajo ya bayar da umarnin ne bayan da mayakan kungiyar suka kashe sama da mutum 40 a wani harin kwantan-bauna da suka kai wa tawagar masu binciken mai na kamfanin NNPC.
Ministan tsaron Nijeriya , Mansir Dan Ali ya ce za a sayi karin kayan aiki na zamani wadanda za su bai wa jami’an tsaro damar ganin abokan gaba daga nesa, don dakile duk wani harin ba- zata na Boko Haram.