A yau Talata ake sa ran mukaddashin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo zai yi wata ganawa da shugabanni daga arewacin kasar a fadar gwamnati da ke birin Abuja.
Kamar yadda Babban mai taimakawa mukaddashin kan harkar yada labarai, Laolu Akande ya bayyana hakan a shafinsa na tweeter, inda ya ce ganawar za ta hada da shugabannin al’ummar Musulmai da kuma na Kiristoci.
Ganawar ba ta rasa nasaba da ci gaba da tuntubar juna da Farfesa Osinbajo ke yi domin a kawo karshen kalaman kiyayya da wasu ke yadawa a kasar.