Bello Hamza" />

Oyegun Zai Ci Gaba Da Zama Shugaban APC Matukar Ba A Yi Babban Taro Ba

Kwamitin zartaswar jam’iyyar APC ta amince da dokar cewa, shugabanin jam’iyyar na yanzu su ci gaba da jagorancin jam’iyar har na shekara daya matukar ba a yi taron jam’iyyar na kasa ba. wannan shawarar da aka zartas ranar Litinin da rana a babban sakatariyar jam’iyyar ta kasa dake Abuja na iya bayar da daman ganin shugaban jam’iyyar John Odigie-Oyegun ya kasance a matsayinsa har bayan zabubbukar da za a gudanar a shekarar 2019.

“In aka samu wani dalilin kasa cika umurnin dokar jam’iyya dana dokokin kasa na gudanar da zabubbuka to sai u koma matsayar kwamitin zartasawar mu a shawarar da suka bayar ranar 27 ga watan Fabrairu 2018, wannan matsaya nasu kuma yana da madogara na musamman a dokokinmu a irin wannan lokacin”

Dabies Ibiamu-Ikanya, shugaban jam’iyyar APC na jihar Ribas ne ya gabatar da kudurin inda gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom ya goyi bayan kudurin yayin da ‘yan kwamitin zartasawr suka amince dashi gaba dayansu.

Har yanzu ba a iya fahintar rashin jin masu kalubalantar wanan tsarin ba duk kuwa da daga dukkan alamu waannan ya taimaka wa Mista Odigie-Oyegun a kokarin da yake yi na tazarce.

Mista Odigie-Oyegun tare da wasu ‘yan majalisar zartaswar sun nemi a kara musu wa’adin shugabanci saboda rikice-rikicen daya addabi wasu reshen jam’iyyar na wasu jihohi. Sun kuma nuna cewa, yin zabe a wasu jihohin zai kara rura wutan rikicin da yake a wasu jihohi abin da kuma zai iya kara kawo wa jam’iyyar matsalolin da zasu iya rusa ta.

Wannan shawara ta ranar 27 ga watan Fabrairu ya samu cikas bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya janye goyon bayansa ga tsarin, inda ya nuna amincewar sa ga yin zabe a dukkan fadin kasar nan. Shugaban kasar ya yi imanin cewar yin zabe zai yi matukar taimakon jam’iyyar daga fada wa rikice rikicen shari’a kafin da kuma bayan zaben gama gari dake tafe.

Mutane na ganin koma baya da shugaban kasar ya yi a kan goyon bayan tazarce kamar mika wuya be ga Bola Tinubu tsohon gwamnan jihar Legasa kuma jigo a jam’iyyar APC wanda ya dade yana neman ganin bayan Mista Odigie-Oyegun a shugabancin jam’iyyar.

Amman wannan shawarar na nuna kamar an sake dawo da shawarar yin zabe ga shugaban jam’iyyar Mista Odigie-Oyegun.

Sauran shawarar da aka yanke sun hada da “ba hukumar INEC wa’adin kwanaki 21 da shari’a ta aiyana na sanarwar zaben da za a gudanar”

 

Exit mobile version