Ozil Baya Tunanin Komawa United –Wenger

Daga Abba Ibrahim Wada

Mai koyar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya ce Mesut Ozil bai damu da rade-raɗin da akeyi ba na cewar zai koma Manchester United da buga wasa.

Wenger ya ce Ozil dan wasan ƙasar Jamus ya maida hankali ne wajen buga wa Arsenal wasanni bai taba barin jita-jitar ta tayar masa da hankali ba kuma shugabannin ƙungiyar sunyi farin ciki da halin girma da dattaku da ɗan wasan ya nuna.

A karshen kakar bana yarjejeniyar Ozil za ta kare a Arsenal, kuma har yanzu bai saka hannu kan tsawaita zamansa a ƙungiyar ba, duk da tuntubarsa da cewa Arsenal ɗin tayi masa tayin ƙarin sabon kwantaragi amma yayi shiru wanda hakan yake nuni da cewa yana shirin barin ƙungiyƙr ne.

Ɗan wasan, mai shekara 29 baya buga abin azo a gani a ƙungiyar tasa a daidai wannan lokaci inda wasu masu sharhi suke ganin kamar yanzu ƙungiyar bata zuciyarsa, shi ya sa ake cewar zai koma Manchester United a watan Janairu.

Ozil ya yi aiki tare da Jose Mourinho a Real Madrid kafin daga baya ya koma Arsenal a shekara ta 2013 kuma ya taimakawa Arsenal ɗin ta lashe kofin ƙalubale na ƙasar ingila har sau biyu.

Ana tunanin dai cewa Manchester united za ta taya ɗan wasan a watan janairu mai zuwa domin gwada Arsenal ɗin ko za ta siyar mata, idan dai Arsenal ɗin bata siyar ba kuma bai saka sabon kwantaragi ba ƙungiyar za ta yi asararsa.

Exit mobile version