Dan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mesut Ozil, ya yi tayin zai biya albashin Jerry Kuy, mai shigar mutum mutumin Gunners da ake kira Gunnersaurus bayan da a ranar Litinin Arsenal ta sanar cewar Kuy wanda shi ne ke shigar mutum mutumin Arsenal shekara 27 yana cikin mutum 55 da aka kora daga aiki a kungiyar.
Arsenal ta fada cewar ya zama wajibi ta rage ma’aikatanta, saboda tabarbarewar tattalin arziki da cutar korona ta haddasa kuma wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya wannan hukunci ya shafa har Jerry Kuy.
‘Yan wasan Arsenal da kociyan kungiyar Mikel Arteta suma sai da suka rage albashi kaso 12.5 cikin 100 a watan Afirilu a lokacin da ake tsakiyar annobar cutar Korona kuma an tsayar da wasanni.
“Na ji bakin ciki da Jerry Kuy, wanda aka fi sani da sunan Gunnersaurus wanda ke kashin bayan kungiyarmu cewar an sallame shi, bayan shekara 27 yana aiki,” in ji Ozil dan kasar Jamus kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a Twitter.
Su ma jami’an kungiyar sai da suka zabtare wani kaso na albashinsu zuwa shekara daya saboda sakamakon bullar annobar cutar Korona tun cikin watan Maris ta sa ana buga gasar Premier League ba tare da ‘yan kallo ba.