Ozil Yana Dab Da Komawa Fenerbahce

Fenerbahce

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Fenerbahce a Turkiya Erol Bulut ya ce lokaci kankani ya rage isowar Mesut Ozil na Arsenal kungiyar domin fara buga wasa karkashin kwantiragin da zai kulla da kungiyar da ke birnin Santambul.

Watanni 10 kenan rabon da Ozil dan asalin kasar  Jamus ya bugawa Arsenal wasa duk da cewa sai a karshen kakar wasan da muke ciki ne kwantiraginsa zai kare ko da ya ke ana sa ran ya bugawa kungiyar wasan karshe gabanin raba gari da ita.

Ozil mai shekaru 32 wanda ya fara buga wasa da Arsenal a shekarar 2013 tun farko kungiyar kwallon kafa ta DC United a Amurka ce ta nemi kulla kwantiragi da shi amma ya zabi komawa kasar Turkiyya da buga wasa.

Ko a zantawar wakilin Ozil Dr Erkut Sogut da manema labarai cikin makon nan, ya tabbatar da cewa makomar dan wasan tsakiyar za ta bayyana ga jama’a nan da kwanaki 7 zuwa 10 masu zuwa.

Ozil wanda ke karbar albashin yuro dubu 350 kowanne mako a Arsenal kocin kungiyar Mikel Arteta ya ce idan har suka cimma jituwar da ta yiwa kowanne bangare dadi a shirye suke su raba gari da dan wasan wanda ya koma Arsenal daga Real Madrid.

Exit mobile version