Connect with us

Nahiyar Afirka

Pakistan Ta Mayar Da Martani Bayan Amurka Ta Soke Tallafin Da Take Bata

Published

on

Ministan harkokin wajen kasar Shah Mehmood, ne ya bayyana haka bayan da ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa ta soke bai wa Islamabad tallafin, saboda kasar ta gaza daukar matakai kan kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke cikin kasar.
Wannan sabon rikici da yake tashi a dangantakar da take kara tsami tsakanin kasashen biyu, yana zuwa ne ana saura kwanaki sakataren hakokin wajen Amurka Mike Pompeo da kuma baban hafsan hafsoshin Amurka Janar Joseph Dunford, su kai ziyara kasar dake kudancin Asiya.
A halin da ake ciki kuma, shugaban hukumar MDD dake tallafa wa ‘yan gudun hijira na falasdiu, ya ce, hukumar za ta ci gaba da tallafawa Falasdinawa, a kuma dai dai lokacin da Amurka ta bada sanarwar kawo karshen gudumawar kudi da take bai wa hukumar.

Advertisement

labarai